Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Mai Dokar Bacci: ‘Yan Sanda Sun Damke Masu Gadi Bisa Laifin Sata

Published

on

Rundunar ‘yan sanda sashen masu yaki da ‘yan fashi da kamami, ta samu nasarar damke wadansu masu gadi a rukunin gidajin Independent Layout Estate da ke yankin Nkwelle Ezunaka cikin karamar hukumar Oyi ta Jihar Anambra, bisa zargin su da laifin sata. An dai bayyana sunayen wadanda a ke zargin kamar haka, Ogbang Clement da kuma Udeh Orji, inda su ka yi wa wani mutum fashin wayarsa da kuma wasu kayayyakinsa. An bayyana cewa, an samu bindiga kirar gida daga hannun wadanda a ke zargin. Kakakin rundunar ‘yan sandar jihar, Haruna Mohammed, shi ya tabbatar da afkuwar lamarin ga manema labarai. Ya bayyana cewa, tawagar ‘yan sandar sashen 33, su ne su ka samu nasarar cafke wadanda a ke zargin.
Mohammed ya ce, “tawagar ‘yan sanda da ke sashe na 33 a garin Onitsha, su ne su ka samu nasarra damke Ogbang Clement dan shekara 34 da kuma Udeh Orji mai shekaru 21. Su dai masu gadi ne a rukunin gidajen Independent Layout Estate, a yankin Nkwelle Ezunaka. “Wadanda a ke zargin dai sun hada kai sannan su ka yi wa wani mutum mai suna Ogbonna Usulor, fashi a yankin Nkwelle Ezunaka, inda su ka kwace masa wayarsa da kuma wasu kayayyakinsa. An dai kwato bindiga kirar gida cike da harsashi da kuma kayayyakin sata daga wurin wadanda a ke zargin.”
Kakakin rundunar ‘yan sanda ya kara da cewa, tawagar ‘yan sanda sashen 33 da ke Onitsha, sun samu nasarar cafke wani mutum mai suna Obi Aledander. Ya ce, si dai Aledander ya hada kai da wani mutum mai suna Felid Ekuneme dan shekara 48, inda su ka sace wata mota kirar Toyota Camry, mallakar wani mutum mai suna Ozoemana Madu da ke zaune a rukunin gidaje na Tobis Estate, a rukunin digaje da ke Holy Trinity Estate. Ya ce, a halin yanzu ya na kokarin samu yadda za a cafke dayan wanda a ke zargi, domin gurfanar da su a gaban kuliya. Mohammed ya tabbatar wa mutane cewa, rundunarsa za ta rage ayyukan ta’addanci a cikin jihar. Ya bukaci mutane su dunga kai rahoto ga ofishin ‘yan sanda a kan duk wani motsi da ba su yarda da shi ba a yankunansu, domin daukan matakin gaggawa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: