Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Mata Ta Kai Karar Uba Bisa Hana ’Yarsu Zuwa Wurinta

Published

on

A ranar Litinin ce, wata mata ma’aikaciya mai suna Misis Grace Obiaje, ta kai karar tsohon mijinta mai suna Raymond gaban kotun, wacce ta ke da zama a garin Jikwoyi, bisa hana yarinyarsu mai shekaru takwas zuwa wurinta.
Obiaje ta bayyana wa kotu cewa, tsohon mijinta ya gaya wa shugabar makarantar da yarinyar ta ke zuwa a kan kar ta sake ta bar yarinyar mai shekaru takwai zuwa wurinta.
“Shugabar makarantar ta hana ni ganin yarinyar lokacin da na je makarantar domin in ganta. Ta bayyana min cewa, mijina ya ba ta doka a kan kar ta sake in ganta. “Ina ta koron ta a kan ta bari in ba yarinyata abinda na saya mata, amma ta ki bari. “Ta tursasa min fita daga makarantar, inda ta rufe kofar makarantar. Na ji takaici sosai,” in ji ta.
Obiaje ta kuma bayyana wa kotu cewa, mijinta ya na mata barazanar zai sa a cafke ta idan har ta dauki yarinyar daga makaranta. Ta na bukatar kotu da ta bai wa mijinta umurnin a kan ya kyale yarinyar ta gudanar da hutun makaranta a wurinta.
Da ya ke kare kansa, Raymond ya musanta dukkan zargin da matar ta ke yi masa, inda ya bukaci kotu ta hana Grace zuwa makarantar yarinyar. “Dukkan abinda ta bayyana wa kotu karka ne kawai ta shirya. Ina rokon wannan kotu mai daraga da ta hana ta zuwa makarantar, saboda duk lokacin da ta je makarantar ta na jan hankalin yarinyar tare da cusa mata wasu dabi’un banza,” in ji shi.
Alkali mai shariya ya shawarci dukkan bagarorin guda biyu da su zauna da junan su lafiya, kar kuma su bata rayuwar wannan yarinya. A nasa hukuncin, Mohammed ya bai wa Raymond umurnin da ya bar yarinyar mai shekaru takwas ta ziyarci mahaifiyarta na tsawan mako biyu a kowani wata. “Kada kowani daya ya hana yarinyar zuwa wurin wani,” in ji shi.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!