Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

’Yan Sanda Sun Ceto Mutum Bakwai Da A Ka Yi Garkuwarsu

Published

on

Rundunar ‘yan sandar Jihar Ogun, ta samu nasarar ceto mutum bakwai wadanda a ka yi garkuwa da su, ciki har da ma’aikatan asibitin Lafiya guda uku, da ke Apata cikin garin Ibadan ta Jihar Oyo. An dai samu rahoton ceto munanen ne ranar 27 ga watan Yuli, a cikin dazuzzukan Fidiwo da kuma Onigari da ke kan babbar titin Legas zuwa Ibadan. An bayyana cewa, an samu nasarar ceto mutanen ne bayan da a ka farauci wasu ‘yan bindiga wadanda a ke kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne wadanda su ka sace ma’aikatan asibiti a ranar 23 ga watan Yuli.
Majiyar ‘yan sanda ta bayyana cewa, Sufeton ‘yan sanda na kasa baki daya, Mohammed Adamu, ya girke jami’an ‘yan sanda a dazuzzukan, inda ya ba su umurnin su cafke masu garkuwan tare da kubutar da duk wadanda su ka sace.
Bayan bayar da wannan umurni, sai kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Bashir Makama, ya bai wa matemakinsa umurnin taimaka wa ‘yan sandar da duk wani taimako da su ke bukata na kayan aiki.
Da ya ke tabbatar da ceto mutunen, kakakin rundunar ‘yan sandar jihar, Abimbola Oyeyemi, ya bayyana cewa, har an mika mutane ga iyakansu. Ya kara da cewa, tawagar ‘yan sanda sun mamaye yankin, inda su ka tursasa wa masu garkuwan sakin wadanda su ka sace sannan su ka gudu. “A nan ne mu ka tabbatar da cewa wadanda a ka yi garkuwa da su su bakwai ne ba su uku ba ne. Mun gano cewa, mutum hudu daga cikin mutanen an yi garkuwa da su ne a ranar 24 ga watan Yuli, amma ba a kawo rahoton lamarin wurin ‘yan sanda ba. Dukka mutum bakwai wadanda mu ka ceto a ranar 27 ga watan Yuli, an mika su ga iyalansu.
“Mun samu nasarar cafke wani daga cikin, wanda mu ke tunanin ya na daya daga cikin masu garkuwan. Ya na taimaka wa ‘yan sanda wajen gudanar da bincike. Mun taba kama mutum 40 daga cikin wannan dajin lokacin da mu ka kai wani samame. Mun samu muyagun kwayoyi daga hannunsu. “Mu na gudanar da bincike. Duk wanda mu ka tarar ya na da hannu a cikin lamarin, to za mu gurfanar da shi a gaban kuliya. Rundunarmu ba za ta huta ba har sai ta tabbatar da cewa ta kawar da ayyukan ta’addanci a cikin Jihar Ogun,” in ji Oyeyemi.
A cikin mutum ukun wadanda a ka yi garkuwa da su ranar 23 a Ibadan, babbar barnin Jihar Oyo, har da Kayode, dan Diraktan asibitin Lafiya da ke garin Apata ckin garin Ibadan, Dakta Oladipupo Sule, a babbar hanyar Legas zuwa Ibadan.
An dai samu nasarar cafke wanda a ke zargin ne a dazuzzukan Fidiwo da Onigari da ke kan titin Legas zuwa Ibadan cikin Jihar Ogun, lokacin da rundunar ‘yan sanda su ka mamaye dazuzzukan tare da tursasa wa ‘yan bindigan gudu daga cikin dazuzzukan
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!