Connect with us

Da dimi-diminsa

Yanzu-yanzu: Jam’iyyar PDM Ta Janye Karar Da Take Yi Kan Gwamnan Bauchi

Published

on

Jam’iyyar Peoples Democratic Movement (PDM) ta janye karar da ta shigar a gaban kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Bauchi, wacce take kalubantar nasarar da ya baiwa Sanata Bala Muhammad zama gwamnan jihar Bauchi bayan zaben 2019 da aka gudanar.

Jam’iyyar ta janye karar ne a zaman da kotun ta gudanar a yau Asabar, inda Lauyan jam’iyyar ya shigar da bukatar neman kotun ta amince musu janye karar da suke yi akan gwamnan jihar Bauchi, jam’iyyar PDP da kuma INEC.

Da yake sallamar karar daga gabansa, shugaban kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar, Justice Salihu Shuaibu ya shaida cewar ya sallami karar ne biyo bayan bukatar janye karar da Lauyan jam’iyyar PDM ya shigar.

Kotun ta amince wa jam’iyyar PDM janye kararsu da suka shigar a gabanta.

Da yake ganawa da ‘yan jarida bayan fitowarsu daga kotun, Lauyan jam’iyyar PDM Barista Aliyu Lemo, ya shaida cewar sun janye karar da suke yi din ne domin su baiwa gwamna Bala Muhammad cikakken dama da ikon ci gaba da gudanar da aiyukan raya jihar ta Bauchi.

Ya ce, ‘ya’yan jam’iyyarsu sun tabbatar musu da cewar gwamna Bala ya zo da kyawawan manufofi na kyautata jihar da samar da ababen more rayuwa wa al’ummar jihar, “A bisa haka muka yanke cewar mu janye kararmu domin bashi damar maida hankalinsa wuri guda wajen ci gaba da aiyukan raya jihar da ya sanya a gaba,” A cewar Lauyan.

A bangaren Lauyan jam’iyyar PDP kuwa, Barista Ben Ubuchi ya jinjina wa matakin da jam’iyyar ta dauka, yana mai bayanin cewar hakan zai ba su damar maida hankali kan karar da ke tsakaninsu da gwamnan jihar da kuma jam’iyyar APC.

Lauyan ya ce sun zo kotun ne domin ci gaba da sauraron karar kwatsam sai suka ji Lauyan jam’iyyar na gabatar da bukatar janye karar da suka shigar, ya bayyana hakan a matsayin karin nasara ga gwamna Bala Muhammad.

Wakilinmu ya labarto cewar, jam’iyyar PDM dai tana zargin INEC ne da kin sanya tambarinta da sunanta a cikin jam’iyyar da suka fafata neman sa’a a zaben 2019 da aka gudanar, a bisa haka ne suka kalubalanci nasarar da Sanata Bala ya samu.

Daga bisani kuma suka janye karar domin baiwa gwamnan cikakken damar ci gaba da gudanar da kyawawan aiyukan da ya sanya a gaba kamar yadda Lauyan jam’iyyar ya shaida wa manema labaru bayan fitowarsu daga Kotun.

Yanzu haka kara guda daya tak ne ke fuskantar Sanata Bala wanda tsohon Gwamnan jihar Bauchi Muhammad Abubakar (APC) ya shigar don kalubantar nasarar da ya kai ga kwace masa iko a jihar.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!