Connect with us

BIDIYO

Sharhin Fim Din ‘Gwani Na Zahra’

Published

on

Suna: Gwani Na Zahra

Tsara Labari: Abdulsalam I. Imam

Kamfani: A. I. Imam Motion Pictures

Shiryawa: Aminu S. Bono

Umarni: Abdulsalam I. Imam

Jarumai: Sadik Sani Sadik, Sulaiman Bosho, Alasan Kwalle, Halima Atete, Tijjani Faraga, Hadiza Muhammed da sauransu.

A farkon fim din an nuna Murtala (Sulaiman Bosho) yana kidaya wasu kudade dake hannun sa, bayan y agama kidayawa sai ya zuba a cikin wata akwatin karfe sannan ya boye ta. Yayin da daga bisani matar sa Tasallah (Halima Atete) ta soma yi masa korafi akan rashin ciyar da iyalan sa gami da barin tad a yunwa da yake yi a koda yaushe.

Murtala ya kasance attajirin mutum mai tsananin son abin duniya, wanda shi da kan sa bay a iya cin dukiyar sa balantana wasu ma su ci, hakan tasa a koda yaushe yana hanyar zuwa gidan abokin sa Badaru (Alasan Kwalle) wanda kullum yake kawo abinci suna ci, a irin hakan ne kuma wata rana abokin nasa Badaru ya nuna masa rashin amincewar sa akan halayen san a mako da son abin hannun wasu, hakan ce tasa suka sami sabani Murtala ya daina zuwa gidan abokin nasa cin abinci.

Wata rana Murtala ya rutsa matar sa yana fada mata cewar an satar masa kudi, yayin day a alkanta satar da dan sa Bala (Sadik Sani Sadik) wanda ya kasance dan shaye-shaye mara jin magana a cikin kauyen, jin an dorawa Bala laifin satar ne sai Tasallah ta nuna wa Murtala cewar it ace ta debi kudi ta sayo omo don wanke kayan sa wadanda suke tsami, nan ta nuna kyamar ta karara akan kazanta da rashin tsaftar mijin nata Murtala.

Kwatsam sai Bala yaje hira wajen budurwar sa Zahra wadda yake son ya aura, amma sai mahaifin ta Mai Kare (Tijjani Faraga) ya nuna cewar ya turo iyayen sa idan hard a gaske auren ta yake son yayi, hakan ne yasa Bala yaje ya sanar da mahaifin sa bukatar sat a zuwa a nemo masa auren masoyiyar sa Zahra, amma sai mahaifin sa Murtala ya nuna cewar aure bai kamaci Bala ba a matsayin san a mutum mara aikin yi, yayin da ita kuma Tasallah ta nuna ta amince Bala yayi aure ko da kuwa kayan dakin ta ne zata siyar ta bada kudin. Bayan Murtala yaje wajen Mai Kare nemowa dan sa aure sai ya soma kushe dan nasa Bala yana nuna rashin ingancin tarbiyyar sa gami da nuna shima bai amince dan nasa ya auri Zahra ba. A sannan ne kuma Zahra ta fito ta kawo wa Murtala abinci, ganin Zahra ne yaji ya kamu da kaunar ta, kuma cikin dan lokaci kadan ya bayyanawa mahaifin Zahra kudirin sa, amma sai mahaifin ta yaki amincewa don yana ganin bai dace a matsayin san a tsoho wanda dan sa yake son Zahra shi kuma ya fito ya nuna yana son taba.

Ko da Murtala ya fahimci cewa bazai samu auren Zahra cikin sauki ba sai yayiwa mahaifin ta romon baka ta hanyar cewar zai bashi kyautar gona. Hakan ne yasa mahaifin Zahra y adage akan sai Zahra ta auri Murtala, yayinda Zahra tare da mahaifiyar ta Talatu (Hadiza Muhammad) suka nuna rashin amincewar su akan auren. Haka shima Bala jin cewar mahaifin sa zai auri Zahra sai ya kamu da bakin ciki. Sai dai kuma bayan Auren ne Zahra taki amincewa da Murtala, wata rana Murtala yaje wucewa sai ya samu labarin mutuwar wani dattijo wanda ya auri budurwar da bata son shi, hakan yasa budurwar ta kasha shi, jin hakan ne yasa Murtala ya soma tsoron kada shima Zahra ta kasha shi, a karshe ma ya sake ta. Sai dai bayan komawar ta gida mahaifin ta y adage akan lallai sai ta koma gidan mijin ta, ko ta bar masa gidan sa, nan mahaifiyar Zahra ta tsara mata tafiya zuwa birni.

Da tsakar dare shi kuma Bala ya shiga dakin mahaifin say a sace akwatin kudin mahaifin nasa, gami da yi masa barazanar zai kasha shi, hakan ne yasa mahaifin sa Murtala ya kyale shi ya tafi, yayin da Bala ya tafi birni wajen wani abokin sa. Sai dai tun akan hanya barayi suka sace akwatin kudin Bala.  Bayan Zuwan Bala wajen abokin sa sai ya tarar da Zahra a gidan a matsayin matar wan abokin sa amma sai Zahra ta nuna sam bata san shi ba, haka suka soma jayayya a cikin gidan, yayin da daga karshe Bala ya hakura da soyayyar Zahra ya amince zai yi aikatau a karkashin mijin ta.

Abubuwan Birgewa:

1. Fim din ya nishadantar, musamman ga masu son kallon fina finai na ban dariya.

2. Camera ta fita radau, sauti ma ba laifi.

3. Murtala (Sulaiman Bosho) yayi kokari sosai wajen nishadantar da mai kallo.

Kurakurai:

1. Sunan fim din wato “Gwani Na Zahra” bai dace da labarin ba, domin ba’a nuna wani tsayayyen masoyin ta wanda ya cancanci sunan ba.

2. Lokacin da Murtala (Sulaiman Bosho) ya fara shiga dakin matar sa da daddare yake gaya mata cewar a matse yake, batsa ta fito karara a cikin kalaman sa shi da matar tasa, domin ko yaro karami zai fahimci inda hirar su ta dosa. Ya dace ayi amfani da salon maganar da mai hankali ne kadai zai fahimta, in har yin wannan hirar ya zama dole kenan.

3. Lokacin da Bala (Sadik Sani Sadik) yaje hira wajen Zahra, an nuna cewar bai gane mahaifin taba, har sai da shi mahaifin ta yace shi ne mahaifin ta, amma bayan ya koma gida don sanar da mahaifin sa azo nema masa auren Zahra, da mahaifin sa Murtala ya tambayi ‘yar gidan waye? Sai aka ji Bala yace ‘yar gidan Buba Mai Kare ce. Shin dama Bala yasan sunan mahaifin Zahra din ne?

4. Lokacin da Murtala (Sulaiman Bosho) ya fara zuwa gidan Mai Kare (Tijjani Faraga) don sanar masa da cewar bai amince dan sa Bala ya auri Zahra ba, me kallo yaga dandazon jama’a ta cikin gilashin idanun dake sanye a fuskar Murtala, duk da kuma an nuna cewar zaune suke a cikin gida  ba’a kasuwa ko dandalin ‘yan siyasa ba.

5. A karshen wakar fim din an nuna wata mace ta dokawa Murtala tabarya aka (Sulaiman Bosho) sai dai kuma ba’a nuna wadda ta doka masa tabaryar ba, haka kuma ko a baki ba’a yi zancen ta ba, ko na dalilin aikata masa hakan, shin wacece? Sannan kuma me kallo yaga Murtala a gidan surikin sa Buba Mai Kare a daren da aka daura auren Murtala din, surikin na sa yana gasa masa raunin da akayi masa da tabarya. Hakan sam bai dace ba domin ba al’ada bace ta malam bahaushe.

6. Kwatsam mai kallo sai yaga Zahra a birni matsayin matar Bash (Aminu Sharif) amma lokacin da Bala yazo birni ya nuna mata sanayya sai ta nuna sam ba ita bace, duk da me kallo yaji mijin ta Bash yana kiran ta da Zee, amma an nuna itama sunan ta Zahra. Ya dace a fahimtar da mai kallo gaskiyar lamarin, idan har ba Zahra bace wadda tayi rayuwa a kauye to ya dace a bayyana hakan karara ko kuma a sake nuna waccan Zahra din ta kauye don fitar da mai kallo daga cikin wasu wasi.

7. Abin daukar sauti ya leko a scene din karshe na fim din.

8. Lokacin da aka kawo Zahra gidan Murtala (Sulaiman Bosho) a matsayin amarya, gabadaya maganganun da su ka yi a cikin dakin batsa tafi rinjaye, wadda kowa zai fahimci abinda suke nufin son aikatawa, musamman a inda Murtala ya ke nuna cewar maganin da ya sha hankalinsa ya tashi bai san yadda zai yi ba sai dai ya watsa ruwan sanyi.

9. Mai kallo yaga Zakari ya kawo budurwar sa gidan wan sa Bash (Aminu Sharif) da nufin su gaisa, kalaman bakin jaruman a nan ma batsa tayi rinjaye, musamman a inda Bash (Aminu Sharif) yake cewa kanin nasa, a ina ya yi wawan kamu haka? Da dai wasu kalaman wadanda basu dace a furta su karara a fili ba.

10. An nuna Bala (Sadik Sani Sadik) ya raina mahaifinsa ya na yi ma sa rashin kunya da abubuwan da basu dace ba, an ce kabi mahaifin ka koda kuwa kafiri ne, don haka duk lalacewar mahaifin sa bai kamata yayi masa abubuwan daya yi masa ba, sai ga shi kuma har fim din ya kare ba’a nuna sakamakon abinda Bala din ya aikatawa mahaifin nasa ba.

Karkarewa:

Babu wani muhimmin sako ko ma’ana wanda fim din yake koyar wa. Haka kuma labarin ya tafi kai tsaye babu doro, sannan kuma fim din zai iya bata tarbiyyar yara kanana da kuma sa jin kunya ga mutanen da su ka kalle shi, domin magidanci ba zai iya kallon fim din tare da iyalansa a cikin gida ba.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: