Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

An Gurfanar Da Direba A Kotu Bisa Farmakin ’Yan Sanda

Published

on

A ranar Talata ce, a ka gurfanar da wani direba mai suna Ibrahim Olarenwaju dan shekara 28 da haihuwa, a gaban kotun Jihar Legas wacce ta ke da zama a garin Ikeja, bisa farmakin wasu ‘yan sanda da dutse da kuma kwalba. Shi dai Olarenwaju ya na zaune ne a yankin Mushin ta Jihar Legas, ya na fuskantar tuhumar hada kai domin aikata laifi, tada zaune-tsaye, farmakan ‘yan sanda lokacin da su ke cikin gudanar da aikinsu da kuma laifin karya doka da oda.

Lauya mai gabatar da kara Aondohemba Koti, ya bayyana wa kotu a ranar Talata cewa, wanda a ke tuhuma ya aikata wannan laifin ne tun a ranar 29 ga watan Yuli, a yankin Dakobiri da ke cikin garin Mushin. Ya kara da cewa, wanda a ke tuhuma tare da wasu mutane sun hada kai wajen tada zaune-tsaye. Koti ya ce, sun tada hankulan mutane sannan su ka farmaki wasu ‘yan sanda wadanda su ke bakin aiki. “Wanda a ke zargi tare da wasu mutane sun karya doka wurin farmakan mutanen yankin Dakobiri, sannan su ka kwace musu dukiyoyinsu.

“Lokacin da ‘yan sanda su ka isa wurin da lamarin ya afku, sai wanda a ke zargi tare da sauran mutanen su ka fara jifar ‘yan sanda da duwatsu da kuma kwalabe. “’Yan sanda sun samu nasarar tarwatsasu, inda su ka cafke wanda a ke zargi, yayin da suran mutanen su ka gudu,” in ji lauya mai gabatar da kara.

Lauya mai gabatar da kara ya cigaba da cewa, wannan laifi ne wanda ya saba wa sashe na 41, 168, 117 da kuma 411 na dokokin manyan laifuka ta Jihar Legas ta shekarar 2015.

Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya ya ruwaito cewa, sashe na 177 ya tanadi hukuncin daurin shekara uku ga duk wanda a ka samu ya farmaki wani dan sanda a lokacin da ya ke bakin aikinsa, yayin da sashe na 411 ya tanadi hukuncin daurin zama a gidan yari na tsawan shekara biyu a duk wadanda a ka samu sun hada kai wajen aikata laifi.

Bayan wanda a ke tuhuma ya musanta laifin da a ke tuhumar sa da shi, alkali mai shari’a Misis M. O. Tanimola, ta bayar da belin wanda a ke tuhuma a kan kudi na naira 50,000 tare da mutum daya mai tsaya masa. Tanimola ta bayyana cewa, duk wanda zai tsaya masa, to ya kasance cikakken ma’aikaci, sannan kuma sai ya nuna shaidar takardar biyan haraji na Jihar Legas na tsawon shekaru biyu. Ta kuma dage sauraron wannan shari’a har sai ranar 9 ga watan Satumba, domin yanke hukunci na karshe.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!