Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

“Na Kashe Mahaifina Ne Saboda Ya Na Son Yin Tsafi Da Ni”

Published

on

Wani matashi mai suna Bisso Aminu dan shekara 40 da haihuwa, ya bayyana yadda ya kashe mahaifinsa mai shekaru 65. Aminu ya bayyana wa rundunar ‘yan sandar Jihar Neja cewa, ya kashe mahaifinsa ne, saboda mahaifin nasa ya na so ya yi tsafi da shi domin ya yi kudi. Lamarin ya faru ne a kauyen Yingu da ke cikin karamar hukumar Rijhau ta Jihar Neja.

Ya ce, “ban taba ladama ba a kan kashe mahaifina da na yi, saboda ya na da mummunar nufi a kaina, ya na so ya sadaukar da ni ga kungiyarsa na asiri. “Na shirya daukar duk wani hukunci. Na riga shi daukar matakin ne, inda na kashe shi lokacin da ya ke yin barci, domin irin mummunar iyyarsa na kashe ni. Wannan lamari dai bai yi masa dadi ba. “Na fahimci yadda mahaifina ya canza min, sannan kuma ya na yawan yi min barazana , na kuma tambaye shi a kan ko na yi masa laifi ne, inda ya ki fada min. “Mahaifina dan kungiyar asiri ne, a bayan nan ne ya yi alkawarin zai sadaukar da nig a kungiyarsa ta asiri, ban da wani zabi sai dai in kashe shi.”

Kakakin rundunar ‘yan sandar jihar, Mohammad Abubakar, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya bayyana cewa, za a gurfanar da wanda a ke zargi a gaban kotu idan a ka kammala bincike.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!