Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Neja: Kotu Ta Daure Malami Shekara Bakwai Bisa Luwadi Da Dalibansa

Published

on

Wata kotu da ke garin Minna ta yanke wa wani malamin makarantar allo mai suna Abubakar Abdullahi dan shekara 33 da haihuwa, hukuncin daurin shekaru bakwai a gidan yari, bisa samun sa da laifin yi wa dalibansa guda 35 luwadi. Shi dai Abdullahi ya na zaune ne a yankin Sabon Gari da ke cikin garin Kontagora, ya na fuskantar tuhumar yin luwadi, wanda ya saba wa sashe na 284 na dokokin fanal kot.

Tun da farko dai, lauyan ‘yan sanda mai gabatar da kara ASP Daniel Ikwoche, ya bayyana wa kotu cewa, kwamandar hukumar Hisbah na karamar hukumar Kontagora mai suna Murtala Abdullahi, shi ne ya kai rahoton lamarin ga ofishin ‘yan sanda da ke garin Kontagora ranar 22 ga watan Yuli. Ikwoche ya kara da cewa, wanda ya kai korafin ya zargi malamin da jan dalibansa guda 35, wadanda shekarunsu bai wuce tara zuwa 14 ba, zuwa cikin dakinsa sannan ya yi musu luwadi a lokuta daban-daban tsakanin watan Maris da watan Yuli. Lokacin da a ka karanta masa karar, ya amsa laifin sa, inda ya bukaci kotu ta yi masa sassauci wajen yanke hukunci. Lauya mai gabatar da kara ya bukaci kotu ta yanke masa hukunci kamar yadda sashe 157 na dokar manyan laifuka ta tanada.

Da ta ke yanke hukunci, alkali mai shari’a Hauwa Yusuf, ta yanke wa Abdullahi hukuncin daurin zama a gidan yari na tsawan shekara bakwai tare da yin bauta mai tsanani.

Da ta ke yanke hukuncin, alkali mai shari’a Hauwa Yusuf ta yanke wa Abdullahi hukuncin zama a gidan yari na tsawan shekara bakai tare da yin bauta mai tsananin yuwa. Mai shari’a Hauwa ta bai wa wanda a ke tuhuma zabi a kan idan ya kammala shekaru hudu a gidan yari, to zai iya biyan tarar naira miliyan biyu a maimakon sauran shekaru ukun da zai yi.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: