Connect with us

MANYAN LABARAI

Yadda EFCC Ta Kwakulo Tsadaddun Motoci 21 A Gidan Yari

Published

on

Jami’ai daga hukumar hana yin ta’annuti da dukiyar gwamnati (EFCC) sun kai wani samame a gidan tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Abdulaziz Yari, wanda ke can garin su, a bisa binciken da hukumar take yi wa gwamnatinsa da ta shude a ranar Litinin.

Jami’an hukumar ta EFCC, baya ga gidan na shi sun kuma bincike gidan kaninsa Jafaru, da kuma na abokinsa Sha’aya Mafara, kaf.

Kimanin tsadaddun motoci na alfarma guda 21 ne jami’an hukumar ta EFCC su ka samu a cikin gidan na Yari, wanda shi ne tsohon shugaban kungiyar gwamnonin kasar nan har zuwa lokacin da ya sauka daga mulki a ranar 29 ga watan Mayu.

Binciken da za a yi wa Yari ne zai tabbatar da ko ta yaya ne ya tara wadannan motocin, in ji wata majiya kamar yanda ta shaidawa wakilinmu.

Yari wanda ba ma shi a cikin kasar nan a lokacin da jami’an hukumar ta EFCC su ka kai wannan samamen a gidan na shi a ranar Lahadi, hukumar dai ta gayyace shi zuwa ofishin na ta.

  Tsohon Gwamnan dai yana kan bincike ne a wajen hukumar a bisa zargin da ake masa na biyan wasu kudade naira bilyan 19 wadanda suka fito daga asusun nan na Faris Klub, naira bilyan 35 da y ace ya kashe a kan hidimar ‘yan gudun hijira, da hana zaizayar kasa, da kuma ta yanda ya Tarawa Jihar bashin naira, 151, 190,477,572.02 a kan ayyukan da ake gudanarwa a cikin Jihar.

Jami’an hukumar ta EFCC da suka zo daga ofishinsu na shiyya da ke Sakkwato, sun iso gidan na Yari ne da ke Talatan Mafara, tare da jami’an na su guda 15. Tun a shekarar 2017 ne hukumar ta EFCC take faman bin gwamnan amma sabili da garkuwar da yake da ita na zama Gwamna sai ta kasa taba shi.

Wata majiya wacce ta nemi a sakaya sunanta ta ce, ìSamamen da jami’an hukumar ta EFCC suka kai a gidan na Yari yana da nasaba da binciken da ake yi ma tsohon gwamnan. Domin akwai wasu abubuwan da ya kamata ya fayyace su na zamanin na shi.

ìYawancin abubuwan duk mutane ma sun san su tun da jimawa, musamman zargin da ake yi masa a kan biyan naira bilyan 19 na kudaden Faris Klub, ga wasu hukumomin tuntuba na NGF, da yanda aka tafiyar da tattalin arzikin Jihar ta Zamfara cikin harkalla.

ìBa cewa muke yi ya aikata laifi ba, amma muna son ya zo ya amsa tambayoyi a kan wasu abubuwa da muka ankarar da shi domin bincike.

Da yake amsa tambaya, majiyar ta kara da cewa; ìAn yarda da a kai irin wannan samamen matukar muna da bayanan sirri mai karfi a kan duk wani dan siyasa.

ìMisali, Jami’anmu sun gano tsadaddun motoci na alfarma har guda 21 a cikin gidan na shi. Sannan muna da zargin da ke nuni da cewa, wani yanki na wadannan kudaden naira bilyan 35 da aka ware wa ‘yan gudun hijira a Zamfara, an yi amfani da su ne wajen siyo tsadaddun motoci.

ìBayanan sirrin da muke da su ne ya sanya Jami’anmu suka binciki gidajen Jafaru Yari, kanin tsohon gwamnan da na abokinsa Sha’aya Mafara. Ai shi kansa kanin na Yari yana cikin gidan na shi a lokacin da Jami’an namu suka kai samame gidan.

ìMaganan ita ce, Yari ya zo ya yi bayani a kan yanda ya sami wadannan motocin masu tsada; ko kuma ya ma bayar da labarin su a cikin bayanan kadarorin sa da ya mallaka, sannan ko bayanin wadannan motocin suna cikin form din da ya cike a lokacin da yake barin ofishin gwamna a watan Mayu.

Da zarar ya yi gamsasshen bayani a kan duk wadannan motocin, EFCC ba ta da wata matsala da Yari, in kuwa bai yi hakan ba, to lallai akwai tambayar da ya kamata ya amsa.

Majiyar ta ce, wasu da a ke zargi su na fuskantar tuhuma a kan kudaden na Faris Klub.

Majiyar ta ce: ìMuna da bukatar Yari da ya zo ofishinmu ya bayyana mana abin da ya sani. Shi ne jigo a kan batun fitar da kudin da duk wata tattaunawa da aka yi.

A yanzun haka, wasu da ake zargi suna cikin tuhuma ne. wasu kadan kuma sun tsere wajen kasar nan. amma tun da dai yanzun Yari ba shi da wata garkuwa da ke kare shi kuma, ya zo ya tantance mana yanda abubuwa su ke. Mu na sa ran zai girmama gayyatar namu ya zo.

Mukaddashin sashen yada labarai na hukumar ta EFCC, Mista Tony Orilade, cewa ya yi, ìDa gaske ne mun je gidan tsohon gwamnan na Jihar ta Zamfara, Yari, a sabili da binciken da ake kan yi.

Kamar yanda a kullum mu ke cewa, ba za mu yi magana a kan duk wani bincike da mu ke yi tare da manema labarai ba.

A lokacin da ya dace, in binciken ya nuna, sai mu ta fi neman hukunci a nan ne sai mu ta fi tare da manema labarai.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!