Connect with us

Da dimi-diminsa

DA DUMI-DUMINSA: Wakilin Jaridar Aminiya Bashir Liman Ya Rasu A Hatsarin Mota

Published

on

Rahotanni sun tabbatar da cewa, wakilin jaridar Aminiya, wacce kamfanin buga jaridu na Media Trust ke wallafawa da Hausa, Malam Bashir Musa Liman, ya rasu a wani mummunan hatsarin mota a kan hanyarsa ta zuwa garin Jama’are na jihar Bauchi a yau Asabar, 10 ga Agusta, 2019.

Wakilin LEADERSHIP A YAU ta samu bayanin cewa, Marigayi Bashir ya gamu da mummunan hatsarin motar ne a karamar hukumar Ningi, inda nan ne asalin mahaifar babansa,j kafin aiki ya kai shi Jama’a.

Bugu da kari, ya na hanyarsa ta zuwa hutun Sallah Babba ne da za a yi gobe, Lahadi, daga Jos, inda a can ne ya aiki a matsayin wakilin Aminiya na jihar.

Yanzu haka ‘yan uwansa na ofishin ‘yan sandan Ningi, domin karbar gawarsa, don yi ma sa jana’iza, kamar yadda addinin Musulunci ya tanada a gobe, wato ranar sallah kenan.

A madadin LEADERSHIP A YAU da daukacin kamfan gungun jaridun LEADERSHIP, mu na mika ta’aziyya ga Media Trust da iyayensa da danginsa. Allah ya sa mutuwa ta zamo hutu a gare shi, Ya kuma bada hakurin jurewa.

Editan LEADERSHIP A YAU, Nasir S. Gwangwazo, ya kara da bayyana Marigayi Bashir a matsayin ma’aikaci mai himma da kwazo, sannan ya yi fatan Allah ya ji kan sa da rahama.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: