Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

‘Yan Sanda Sun Kame Mutanen Da Ke Tseguntawa Masu Garkuwa Labari

Published

on

A shekaran jiya Alhamis ce, rundunar ‘yan sandan birnin tarayya ta samu nasarar cafke wasu mutane da ke tseguntawa masu garkuwar da suka addabi mutanen karamar hukumar Abaji da kewaye.

Kwamishi nan ‘yan sanda mai kula da shiyyar, Mista Bala Ciroma, ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai a Abuja.

Ya ce, mutum biyar din da suka kama, na ci gaba da yi wa ‘yan sanda bayanan da za su taimaka wajen gano wadanda suke hada kai da su, suke aikata laifuka.

Kwamishinan ya bayyana cewa, mutum biyar din da aka kama, ya nuna kokarin da rundunar ‘yan sandan ke yi na yaki da masu garkuwa a wannan yankin.

Ciroman kuma ya ci gaba da cewa, rundunar ‘yan sandan ta musamman da ke yaki da ‘yan fashi da makami ta kama wasu rikakkun ‘yan fashi guda shida.

Haka kuma ya ce, an cafke wasu masu laifin da suka kware da ke satar kudi a bankin ta hanyar layin waya a Keffi ta jihar Nasarawa.

Ciroma ya ce, masu laifin na bin sawun asusun ajiyar banki ta hanyar layin waya su kwashe wa mai katin kudi a banki.

“Idan suka yi amfani ta layin sai su kutsa su gano lambar asusun ajiyar da ita kuma za su yi amfani wajen yin katin ATM wanda da shi ne za su dinga cire kudin.

“Shugaban barayin yana amfani da katin wajen cire dukkan kudin da aka  tura cikin wani asusun daga asusun da suka yi masa kutsen” in ji shi.

Ya ce, daga cikin abubuwan da aka samu a wurin barayin sun hada da  wayoyi guda 13 da layuka guda, 55 da kuma katin ATM guda 6.

Kwamishin ya kara da cewa, a wani farmaki da suka kai ranar 30 ga watan yuli,sun kama wani dan shekara 40 da kera bindida a kauyen Kuloda ke karamar hukumar Abaji.

Ya ce an kama masu laifin ne sakamakon binciken kwakwaf da aka yi wa wasu da aka kama su da bindiga guda biyu cikin ‘yan fashin da aka kama.

Haka kuma Ciroman ya ce, an kama wasu ‘yan uwan juna mutum biyu da ke ba ‘yan fashin magani.

Abubuwan da aka samu wajen wadanda aka Kaman su ne, bundigar gargajiya guda bakwai da layu da guraye da kuma kayan balle kofa.

Ya ce, rundunar ‘yan sandan kuma ta kama wasu mutum uku da mota kirar Toyota Camry wadda ake zargin sun sato ta ne daga jihar Kebbi.

Ya ce nan ba da jimawa ba, za su mika wadanda ake zargin ga rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi domin ci gaba da gudanar da bincike.

A karshe, kwamishinan ya ce, sauran wadanda aka kama su rundunar za ta kai su koto bayan sun gama bincike.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: