Connect with us

RAHOTANNI

Dan Majalisar Tarayyar Birnin Kano Ya Yi Rabon Ragunan Layya

Published

on

Dan majalisar tarayya mai wakiltar karamar hukumar birnin Kano shugaban kwamitin tsaro. Alhaji Sha’aban Ibrahim Sharada ya raba dabbobi ga al’ummar mazabarsa domin yin layyar babbar sallah.

Rabon dabbobin da yawanci shugabanin jam’iyyar APC na karamar hukumar suka amfana dashi ya hada da shanu da kuma raguna daya bayar ga matakin mazabu da karamar hukumar da dattawa da yan kwamitoci.

Cikin wadanda suka sami kyautar dabbobin sun hada da kunshin shugabannin jam’iyyar APC na karamar hukumar birni su 27 da aka basu sa guda daya.Haka suma kunshin  shugabanni na mazabu 13 kowace mazaba ta sami sa guda.

Dan majalisar na tarayya mai wakiltar birnin ya kuma baiwa dattawan jam’iyya na yankin sa guda sannan yan kwamitin yan uku na mazabun karamar hukumar 13 raguna.

Suma yan gidan shekarau sardaunan Kano da suka shigo APC daga PDP dan majalisar ya basu sa guda.Sannan ya baiwa dukkan wadanda ya baiwa shanun kudin fida.

Saidai wata majiya daga cikin shugabannin APC a karamar hukumar birnin daya nemi a sakaya sunansa yace akwai wasu daga jagorori a yankin da suka nemi yan jam’iyyar karsu karbi kyautar dabbobin na dan majalisar hakan na faruwane kuwa sakamakon rashin jituwa da ake jin akwai a tsakanin jagororin da dan majalisar Sha’aban Sharada.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!