Connect with us

RAHOTANNI

Abubakar Sadik Ya Zama Sarkin Fadar Matawallen Zazzau

Published

on

A ranar juma’ar da ta gabata, Mutawallin Zazzau Dokta Muhammad Aminu Ladan Sharehu ya nada Alhaji Abubakar Sadik sarautar Sarkin Fadarsa, wanda taron nadin da ya gudana a kofar gida tsohon Mutawallin Zazzau, marigayi Shekh Ladan Sherehu ya sami halartar al’umma da suka fitattun mutane a ciki da wajen lardin Zazzau.

A sakonsa a wajen nadin Sarkin Fadan Mutawallin, mai martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris, ya jawo hankalinsa da ya ci gaba da rike amanar Mutawallin Zazzau, na wannan dama da ya ba shi, na sarautar Sarkin Fadansa fiye da yadda ya ke yi a baya.

Mai martaba Sarkin Zazzau, wanda Wakilin Sana’a na Zazzau Alhaji Buhari ya waiklce shi a wajen nadin, ya kuma kara da jawo hankalin sabon Sakin Fadan da aka nada day a ci gaba da zama mai tunani yin koyi da Mutawallin Zazzau, na yin amfani da damar da Allah ya tabbatar ma sa da shi, na Sarkin Fadan Mutawallin Zazzau, wajen tabbatar da zaman lafiya a masarautar Zazzau da kuma tallafa wa rayuwar matasa a bangarorin ci gaba da neman ilimi da kuma sana’o’in dogaro da kai, fiye da yadda ya ke yi a baya.

A  jawabinsa jim kadan bayan ya kammala nadin Sarkin Fadansa, Mutawallin Zazzau, Dokta Muhammad Aminu Ladan Sherehu, ya fara da cewar, ya nada Alhaji Abubakar Sadik wannan sarauta ce, domin halinsa nagari day a shafi amana da kuma biyayyar da ya ke yi ma sa a shekaru da dama da suka gabata.

A nan sai Mutawallen Zazzau ya yi kira gareshi da ya ci gaba da wadannan halaye na sa, na amana da kuma biyayya tare da yin fice wajen tallafa wa matasan da suke kusa ko kuma nesa da shi.

A zantawar da wakilinmu ya yi da Sarkin Fadan Mutawallin Zazzau Alhaji Abubakar Sadik jim kadan kammala nadinsa, ya nuna matukar jin dadin da kuma godiya ga mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris, na baya ga amincewar day a yi da ya yi a yi na ba shi wannan sarauta har kuma ya turo Wakuilin Sana’a na Zazzau ya wakilce a wajen wannan nadi da Mutawallin Zazzau ya tabbatar ma sa da shi a wannan rana.

Sarkin Fadan Mutawallin Zazzau, Alhaji AbubakarSadik ya kuma mika godiya ta musamman ga mai girma Mutawallin Zazzau Dokta Muhammad Aminu Ladan na wannan dama da ya ba shi, y ace, wannan wani kaimi ne Mutawallin Zazzau ya yi ma sa, da zai kara tashi tsaye wajen aiwatar da abubuwan da za su tallafa wa matasa da kuma ci gaba da bayar da duk gudunmuwar da zai iya domin kara samar da zaman lafiya a masarautar Zazzau da jihar Kaduna da kuma Nijeriya baki daya.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!