Connect with us

LABARAI

Gwamnatin Koriya Ta Jinjinawa Gwamnan Zamfara Bisa ‘Yanto ‘Yan Kasarta Daga Hannu Masu Garkuwa

Published

on

Gwamnatin kasar Koriya ta jinjinawa gwamnan Zamfara, Dk. Bello Matawalle bisa ‘yanto ‘yan kasarta Likitoci daga hannun masu garkuwa. Rahotanni sun bayyana cewa; Dk. Jeng Sunail an sace shi ne a babban Asibitin Tsafe zuwa maboyar da ba a sani ba, inda aka tsare shi har na tsawon wata shida.

Wannan bayanin jinjinawar na fitowa ne daga Malam Zailani Bappa, babban mashawarci na musamman ga Gwamnan kan harkokin wayar da kan jama’a da sadarwa a wata sanarwa da ya fitar a garin Gusau a ranar Lahadi. Inda ya tabbatar da cewa; sakon gwamnatin Koriya ya iso ne ta hannun Jakadanta a Nijeriya, Jon Tong Chol.

Jon Tong Chol ya tabbatarwa da gwamnan cewa; gwamnatin Koriya ta samu labarin sakin ‘yan asalin kasarta wanda aka yi ba tare da biyan kudin fansa ba. Inda ya ce lallai wannan abin jinjinawa ne.

Sanarwar ta ce a lokacin da yake karbar bakuncin Jakadan, Gwamna Matawalle ya tabbatar da cewa; gwamnatin na su za ta tabbatar da ta ci gaba da kare rayukan al’umma da dukiyoyinsu ciki harda bakin da ke jihar.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: