Connect with us

KASUWANCI

Hukumar Kwastom Ta Kama Buhunan Shinkafa Na Miliyoyin Naira A Neja

Published

on

Hukumar yake da cin hanci da yiwa tattalin arzikin Nijeriya zagon kasa EFCC  ta shiyyar reshen jihar Neja ta cafke  motoci dauke da buhunan shinkafa ta kasar waje da a ke zargin cewa an shigo da su ne ta barauniyar hanya.

Jami’an hukumar sun tare motar dauke da da buhuna 1, 940 na shinkafar waje da a ka yi fasa kaurin da kudn su ya haura miliyoyi.

Shugaban hukumar na shiyyar jihar ta Neja, Abba-Kassin Yusuf ne ya sanar da hakan gay an jarida a ranar larabar data wuce a cikin jihar Neja.

Ya kara da cewa, jami’an hukumar sun kama motoci ne a wurare daban-daban.

A karshe ya ce, a garin Mokwa an tare wata mota dauke da buhunan shinkafa 520 da kuma buhunan sukari  ta barauniyar hanya.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: