Connect with us

KASUWANCI

Lantarki: EFFC Ta Fara Bincikar Gwamnatin OBJ Kan Dala Biliyan 16

Published

on

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa da yiwa tattalin arzikin Nijeriya zagon kasa EFCC, ta fara bincike kan shirin samar da wutan lankarki da ya lashe dala biliyan sha shida a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo.

Sai dai, an samu banbancin ra’ayi kan takamamen adadin kudin kwangilar samar da wutan lantarkin inda wasu suka ce dala biliyan  sha shida ce wasu kuma sun hakikance dalla biliyan 13.8 ne.

Bugu da kari, an kuma ruwaito cewa, akwai yiwuwar hukumar ta EFCC za ta kama wasu daga cikin muhimman wadanda suke da hannu cikin kwangilar da aka cigaba da yin ta har zuwa mulkin marigayin tsohon shugaban kasa marigayi Alhaji  Umaru Yar’adua da Goodluck Jonathan.

Har ila yai, an kuma ruwaito cewa za a gayyaci wasu manyan ma’aikatan gwamnati sha takwas da su kayi murabus da tsaffin ministoci biyu domin amsa tambayoyi a  kan kwangilar.

Haka kuma, akwai yiwuwar hukumar ta EFCC ta gayyaci wasu manyan jami’an babban bankin Nijeriya CBN domin suma su amsa tambayoyi.

A cikin Yulin 2019 ne majalisar wakilai na tarayya ta cimma matsayar gudanar da bincike kan makuden kudaden da gwamnatin tarayya ta kashe kan kwangilar na magance matsalar samar da ingantaccen wutan lantarki a daukacin fadin Nijeriya.

Idan za a iya tunawa, a baya tsohuwar gwamnatin Obasanjo ta ce ta kashe makudan kudi a fannin samar da lantarkin domin samar da karfin wuta kimanin megawatts dubu 40 a shekarar 2020.

Ya yanzu, sassan Nijeriya da dama ba a cika masu  wannan alkawarin da aka yi musu na samar da hasken wutar lantarkin isashe ba duk da cewar,an kuma ware kudade saboda aikin, hakan ya sa gwamnati mai ci yanzu za ta binciki yadda aka kashe kudaden.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: