Connect with us

KASUWANCI

Mu Na Bin Kanawa Bashin Naira Biliyan 148 – KEDCO

Published

on

Kamfanin da ke tura wutar lantarki KEDCO ya yi shelar cewa, yana bin alumar jihar Kano bashin har na zunzurucin naira biliyan biliyan 148 na kudin wutar lantarki da suka sha suka kima ki biyan kamfanin,

KEDCO ya kuma roki alummar jihar su sauke nauyin basin dake a kansu na kamfanin yadda kamfanin zai samu sukunin gudanar da ayyukansa yadda ya dace.

Kamfanin na KEDCO ya sanar da haka ne ta hanyar shugaban sadarwarsa Ibrahim Sani Shawai a ranar Talatar data gabata.

Ibrahim Sani Shawai ya ci gaba da cewa, matsalar da suka samu da kamfanin rarraba wutar lantarki na TCN, ya na da alaka da rashin biyan kudin wata-wata da masu amfani da wutar suka ki biyan kamfanin na KEDCO.

Ya kara da cewa, bisa yanayin cigaba da kamfanin yake yi, kamfanin zai samu wata garkuwa idan har al’ummar jihar ta Kano suka biyasu bashinsu.

Ya sanar da cewa, karin samuwar wutar lantarkin ta ta’allaka ne akan masu amfani da wutar.

A cewar sa, binciken da suka gudanar sun sun gano ya tabbatar da gano bashin naira biliyan 148, da kamfanin na  KEDCO ta ke bin masu amfani da wutar lantarki a jihar.

A karshe ya ce, duk da bashin da suke bin alumar jihar kamfanin bazai gazaba ba, wajen tabbatartuwa samun ingancin wutar lantarkin a jihar.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: