Connect with us

LABARAI

Sallar Idin Layya: Malamai Sun Shawarci Matasa Da Su Guji Tukin Ganganci

Published

on

Alhaji Muhammadu Abubakar, Limamin babban Masallacin Bwari dake Abuja ya gargadi matasa da su guji yin tukin ganganci da ababen hawansa musamman a lokacin bukukuwan sallar idin layya. Alhaji Muhammadu Abubakar, ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi a yayin ganawarsa da manema labarai a birnin tarayya Abuja.

Limamin ya mika godiyarsa ga Allah da ya nuna mana wannan sallar lafiya, inda ya yi addu’ar Allah yasa a yi bukukuwan sallah lafiya. Tare da neman matasa su guji karya dokokin kasa wajen gudanar da bukukuwansu. Sannan ya shawarce su da su kasance masu bin doka da oda.

Ya kara da cewa masu guje-guje a ababen hawa da sunan murna su guji hakan saboda hatsarin da ke ciki.

Shima Madawakin Sarkin Bwari, Alhaji Muhammadu Ango, wanda ya yi bayani a madadin Sarkin Bwari, Alhaji Isah Ijakoro, ya yi addu’ar Allah ya dawo da mahajjatanmu lafiya.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!