Connect with us

RAHOTANNI

Shagalin Sallah A Baya Da Yanzu – Sharif Usmaniyya

Published

on

An ce duniya ba ta lalace ba, a kullum ma kara ma ta ado a ke yi, sai dai mutanen cikinta ne sukan lalata kansu. Kusan komai ka dako yadda iyayenmu suke yinsa a zamanin baya, sai ka ga bambancinsa da yanda muatanan mu na yanzun su ke yin sa, a kullum kuma sai ka taras da na iyayen nan namu shi ne mafi tsafta. Kamar haka a lokaci irin wannan na shagulgulan Sallah, in ka sami dattawa sun aba ka labarin yanda ake gudanar da shagulgulan Sallah a zamanin baya, sai ka ji don me ba za mu koma kamar na bayan ba.

A kan haka ne, wani dattijo mai suna Sharif Abubakar Usmaniyya, da ke garin Kaduna ya dan zayyano mana da yanda ake bukin Sallah a lokutan baya, ya kuma kwatanta da abin da ake yi a halin yanzu, sannan ya bayar da shawarwari musamman ga iyaye a kan yadda ya kamata su kula da ‘ya’yansu a wajen shagulgulan na Sallah.

Sharif Abubakar Usmaniyya ya ke cewa, ìIdan mutum ya ce zai kwatanta yanda ake shagulgulan Sallah a baya da kuma yanda ake yi a halin yanzun, zai ga cewa tamkar a baya ne ake yin shagulgulan Sallah, amma a halin yanzun a kan dai je Idi ne a dawo kawai. A baya tun a na cewa Sallah ta rage saura kwanaki Bakwai misali, kowa zai ga alami na Sallah ta karato. Hatta yara a wancan lokacin kowane yaro da zaran Sallah ta karato zai yi asusu inda zai ta ajiye dan taro da sisin da yake samu yana tarin hidimar Sallah. Amma a halin yanzun wani ma sai ka tambaye shi yaushe ne Sallah din bai sani ba, in ba ya rage kwanaki biyu ko uku ba, shi ma ya ji mutane ne suna magana.

A nan kamar yanda a kan sami samari masu hankali, da dattijai masu hankali suna yin kira a kullum a kan a daina yin abubuwan nan guda uku. Wanda na farko shi ne buga wannan Nok’awut din da ake yi, domin buga wannan abin ya kan taimakawa wasu batagari ne su shigo cikin mutane suna yin barna da sace-sace irin na fashi da makami domin sau tari ba ka iya rarrabe karan wannan abin da kuma karan bindigar gaske.

A nan tilas ne mu yi wa gwamnatocin Kano, Kaduna, Katsina Sakkwato da duk sauran Jihohin da suka yi hani a kan buga wannan Nok’awut din da duk wasu ma wasanni da taruka marasa kyau a lokacin shagulgulan na Sallah.

Ya kamata a rika daukan matakai a kan duk wani yaro da aka kama yana buga wannan Nok’awut din har ma da iyayensa a dauki mataki a kansu ta yanda hakan zai zama darasi a kan saura a nan gaba. Ina jan kunnin iyayen yara da su hana yaran na su kudin da za su je suna siyan wannan abin suna bugawa, in kuma har za a baiwa yaron kudi domin ya je ya sayo cingam ko minti ko biskit da makamantansu, to ya kamata a ja masu kunni sosai kan kar su suna siyan wannan abin.

Masu guje-guje kuma da ababen hawa ya kamata a yi masu hani, hukuma kuma ta sanya ido sosai a kansu, a Sallar bara a nan Kaduna mun ga inda wasu yaran suka halaka kawukansu a sabili da irin wannan guje-gujen na rashin hankali.

Don haka, ya kamata mu iyaye a kullum mu kasance masu kwakkwafawa da gyara halayyar yaranmu, mu rika ja wa ‘ya’yanmu kunni a kan duk irin wadannan abubuwan da ba su kamata ba. Wadannan iface-iface da guje-gujen da ake yi sam ba su ne murnar Sallah ba, hanyoyin yin murnar Sallah su na da yawa.

Yana da kyau kuma iyaye har ila yau su yi gyara a kan abin da ake cewa yawon Sallah da yara ke zuwa, ta yanda zai kasance da gaske ziyara din ce ta sada zumunci. A yanzun yawon Sallah sau tari ya zama na shaye-shaye ne, za ka ga gungun yara sun taru suna kunna wiwi, su na shan sholisho ko maganin barcin nan da makamantansu, ba ma za ka tsammaci ga abin da suke yi ba, sai dai kawai a dan lokaci kadan ka ga sun fita hayyacin su, daganan ne kuma sai ka ga fitina ta tashi domin sun fita daga cikin hayyacin su.

Ya kuma kamata iyaye su kula musamman iyayen yara ‘yan mata wadanda sukan caba ado wasu ma dakunan samari za su nufa da sunan wai yawon Sallah, wanda sam wannan bai halasta ba, a ce wata yarinya komai kankantarta, komai girmanta a ce ta yi adon Sallah ko ma ba na Sallah din ba ta tafi dakin saurayi da sunan yawon Sallah ko wani abu na daban. Wannan sam-sam bai dace ba, Addinin Musulunci ma bai yarda da wannan ba. Saboda haka, iyaye su ja wa ‘ya’yayensu mata, musamman wadanda suka fara mallakan hankalinsu  da su guji zuwa yawon Sallah a wajen samari.

A karshe, muna kara yin kira ga hukumomi da su kara sanya ido a duk wurare na musamman da wuraren taruwan jama’a domin tabbatar da batagari ba su kai ga aikata abubuwan da suka sabawa doka da oda ba. Domin idan jami’an tsaro su na wuraren to ko ba kamawa su ke yi ba, kasantuwarsu a wajen zai sanya masu son yin barnarsu shiga taitayinsu. Sannan su rika tsawatarwa a kan duk abin da suka gani wanda bai dace ba.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: