Connect with us

LABARAI

Tsaro: Sarkin Kano Ya Jinjina Wa Gwamna Ganduje

Published

on

A jiya Lahadi ne, ranar da al’ummar Musulmi suka gudanar da bikin Sallah Babba a Jihar Kano, Mai martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II, shi ne ya yi limancin Sallar Idin bana wadda aka gudanar a filin Idin Kano da ke kofar Mata, a kwaryar birnin ta Kano.

Bayan Kammal Sallar Idin ne kuma, Sarkin Kanon kamar yadda ya saba bisa al’ada bayan kammala huduba, ya koma ta kofar  Kwaru gaban gida Shettima, inda ya gabatar da jawabin barka da Salla ga dimbin al’ummar Jihar Kano, ciki kuwa har da Gwaman Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, wanda ya samu rakiyar manyan-manyan Jami’an Gwmnati, inda suka hallara a gidan Shettima, aka kuma saurarin jawabin barka da Sallar daga bakin Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II.

Malam Muhammadu Sanusi II, ya jinjinawa Gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje bisa kokarinsa na tabbatar da tsaro a fadin Jihar Kano baki daya. Haka kuma, Sarkin ya bukaci Gwamnatin Kano, da ta samar da isasshen Takin-zamani da sauran abubuwan da za su inganta harkokin noma a Jihar Kano.

Haka zalika, Mai Martaba Sarkin, ya kuma bukaci al’ummar Kano da su ci gaba da gudanar da addu’o’in neman dorewar zaman lafiya a fadin Jihar ta Kano da ma Kasa baki daya, daga nan ne kuma sai Sarkin ya bukaci sauran al’umma, da su kara himmatuwa wajen baiwa Jami’an tsaro irin hadin kan da ake bukata.

A karshe, Malam Muhammadu Sanusi II, ya ja hankalin al’ummar Kano, da su kara kaimi wajen rungumar harkokin Alluran Rigakafin cututtukan da ke kashe kananan yara da mata a lokutan haihuwa. Mai Martaba Sarkin, ya yi addu’ar fatan Allah Ya nuna mana Sallar badi da ta badin -badada lafiya.

Har ila yau, cikin Hakiman da suka halarci Sallar Idin Babbar Sallar ta bana, akwai Madakin

Kano, Hakimin Dawakin Tofa, Makaman Kano, Hakimin Wudil, Galadiman Kano, Walin Kano, Hakiman Gabasawa, Rimin Gado, Garko da sauran su duk sun halarci bikin wannan Sallah, wanda ya gudana a jiya.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!