Connect with us

WASANNI

Van Dikj Zai Iya Zama Gwarzon Duniya – Robben

Published

on

Tsohon dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid da Bayern Munchen, Srjen Robben, ya bayyana cewa dan wasan tawagar kasar Holland, Birgil Van Dikj, zai iya zama gwarzon duniya na wanann shekarar ta hanyar doke ‘yan wasa Ronaldo da Messi.

‘Yan kwallon kungiyar kwallon kafa ta Liverpool, Birgil Van Dijk da Mohamed Salah da kuma Sadio Mane suna daya daga cikin ‘yan wasa 10 da za a fitar da gwarzon dan kwallon kafa na Vana kamar yadda hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa, ta fitar.

Sauran ‘yan wasan sun hada da dan wasan Tottenham Harry Kane da tsohon dan kwallon Chelsea Eden Hazard wanda yanzu yana Real Madrid, sai Lionel Messi da Cristiano Ronaldo da fitaccen dan wasan Paris St Germain Kylian Mbappe.

Sauran cikon goman sun hada da Frenkie De Jong wanda yabar kungiyar kwallon kafa ta Ajad zuwa Barcelona  da kuma dan wasan baya, Matthijs De Ligt, wanda shima ya koma Juventus daga Ajad din.

“A kakar wasan data gabata ya lashe gasar cin kofin zakarun turai wadda kusan a yanzu itace gasar da ake dubawa kafin a bawa mutum kyauta kuma sannan yayi na biyu a firimiyar Ingila saboda haka ina ganin ya cancanta” in ji Robben, wn=anda ya taba buga wasa a Chelsea.

Daga Vangaran masu koyarwa kuwa kociyoyin kungiyoyin kwallon kafa ta Liverpool Jurgen Klopp dan kasar Jamus, dana Tottenham Mauricio Pochettino, dan asalin kasar Argentina wadanda suka kara a wasan karshe a kofin zakarun turai suna cikin takarar wanda ya fi taka rawar gani wajen koyarwa.

Shi ma mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Manchester City Pep Guardiola, dan asalin kasar Sipaniya, wanda ya lashe kofi uku a Ingila har da gasar firimiya yana cikin takarar kocin da babu kamarsa a Vana.

Sauran  masu koyarwar da ke yin takara sun hada da kocin Algeria, Djamel Belmadi da na Faransa, Didier Deschamps sai kuma mai horar da kungiyar Riber Plate ta kasar Argentina, Marcelo Gallardo da kocin kasar Peru, Ricardo Gareca da na Portugal Fernando Santos da na Ajad Erik Ten Hag da na Brazil, Tite, wanda ya lashe Coppa America.

Za a fitar da zakaran Vana ta hanyar zabe da masu kallon kwallon kafa sau da kafa za su yi da ‘yan jarida da masu horar da tawagar kwallon kafa ta kasa da kasa da kyaftin-kyaftin dinsu kuma za a yi bikin karrama gwarzon Vana a birnin Milan ranar 23 ga watan Satumba.

Masu takarar Gwarzon dan kwallon kafa na duniya a 2019:

1. Birgil Van Dijk, Netherlands

2. Sadio Mane, Senegal

3. Mohamed Salah, Egypt

4. Harry Kane, England

5. Cristiano Ronaldo, Portugal

6. Lionel Messi, Argentina

7. Matthijs de Ligt, Netherlands

8. Frenkie de Jong, Netherlands

9. Kylian Mbappe, France

10. Eden Hazard, Belgium

Masu takarar gwarzuwar ‘yar kwallon kafa ta duniya a 2019:

1. Lucy Bronze, England

2. Julie Ertz, United States

3. Caroline Graham Hansen, Norway

4. Ada Hegerberg, Norway

5. Amandine Henry, France

6. Sam Kerr, Australia

7. Rose Labelle, United States

8. Bibianne Miedema, Netherlands

9. Aled Morgan, United States

10. Megan Rapinoe, United States

11. Wendie Renard, France

12. Ellen White, England

Gwarzuwar/gwarzon mai horarwa da ’yan wasa mata a 2019:

1. Phil Nebille, England

2. Jill Ellis, United States

3. Milena Bertolini, Italy

4. Peter Gerhardsson, Sweden

5. Futoshi Ikeda, Japan

6. Antonia Is, Spain

7. Joe Montemurro, Arsenal

8. Reynald Pedros, Lyon

9. Paul Riley, North Carolina Courage

10. Sarina Wiegman, Netherlands

Gwarzon kocin da yafi taka rawar gani a 2019:

1. Jurgen Klopp, Liverpool

2. Pep Guardiola, Manchester City

3. Mauricio Pochettino, Tottenham

4. Djamel Belmadi, Algeria

5. Didier Deschamps, France

6. Marcelo Gallardo, Riber Plate

7. Ricardo Gareca, Peru

8. Fernando Santos, Portugal

9. Erik Ten Hag, Ajad

10. Tite, Brazil
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: