Connect with us

LABARAI

Yaki Da Ta’addanci: Gwamna Zulum Ya Bukaci ‘Yan Nijeriya Su Yi Wa Sojoji Addu’a

Published

on

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum ya bukaci ‘yan Nijeriya da su yiwa sojoji addu’a na musamman domin samun nasarar yaki da ta’addanci musamman a arewa maso gabashin Nijeriya.

Farfesa Zulum ya bayyana hakan ne a sakon da ya isar na sallar idin layya a garin Maiduguri a ranar Lahadi wanda Malam Isa Gusau mai ba gwamnan shawara kan harkokin hulda da jama’a ya fitar.

Gwamnan ya bukaci a gudanar da addu’o’i na musamman domin wanzuwar zaman lafiya da hadin kai a kasarnan. Gwamnan ya ce; sallar idin layya na tuna mana ne da sadaukarwa ne da kuma tsoron Allah da da’a ga Allah, ya ce; ya kamata al’umma su yi amfani da wannan dama wajen yiwa sojoji addu’a.

Ya ci gaba da cewa; akwai sojoji da jami’an ‘yan sanda, da na DSS da ‘yan sa kai da CJTF da maharba wadanda suke yaki da ta’addanci a jihar kuma suka bar masoyansu da ‘yan’uwansu domin tabbatar da al’umma sun yi bikin sallah cikin zaman lafiya, inda ya yi fatan suma a yi musu addu’a domin su samu nasara a yakin da suke yi da ta’addanci.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!