Connect with us

RAHOTANNI

‘Yan Takarar APC Sun Nemi Buhari Ya Tsame Hanunsa Kan Rikicin Majalisar Bauchi

Published

on

Kungiyar ‘yan takarar majalisar dokokin jihar Bauchi a zaben 2019 a karkashin jam’iyyar APC, sun roki shugaban kasa Muhammadu Buhari da kada ya tsunduma kansa cikin rikicin shugabancin majalisar dokokin jihar Bauchi domin tabbatar da mulkin demokradiyya.

A wani taron menama labaru da suka gudanar a karshen mako a Bauchi, mambobin kungiyar sun shaida cewar a matsayinsu na wadanda suka nemi damar shiga majalisar Allah bai yi ba, sun tabbatar da matakin shawo kan rikicin da aka bi a daidai wannan gabar, mataki ne wanda ya dace, suna masu tabbatar da cewar sauran ‘yan majalisun jam’iyyar APC 17 din ma sun je an rantsar da su a cikin kwaryar majalisar, don haka ne suka nemi Buhari ya kyalesu domin tabbatar da shugabanci na kwarai.

A takardar bayan taro da suka gabatar wa ‘yan jarida, wanda shugaban kungiyar Muhammad Aliyu ya karanta, sun nemi Buhari ya gane cewar yanzu haka shugaban majalisar jihar ta Bauchi dan jam’iyyar APC ne, don haka ne suka nemi a bar majalisar ta ci gaba da gudanar da aiyukanta domin kyautata shugabanci a jihar.

Takardar bayan taron, ta kuma zargi tsohon gwamnan jihar Bauchi, Muhammad A. Abubakar da kitsa dukkanin tashin hankalin da ke faruwa a majalisar jihar a halin yanzu, suna masu shaida cewar tun a farkon lokacin zaben fitar da gwani ma shine ya fara dagula wa jam’iyyar lamura a jihar, suna masu neman shugaba Buhari ya san da wadannan, “Shi tsohon gwamnan shine ke ingiza tsohon Kakakin majalisar dokokin jihar, Kawuwa Shehu Damina domin ya kalubanci gwamna mai ci, Sanata Bala Muhammad na jam’iyyar PDP,” A cewar su.

“Muna cike da farin cikin kawo karshen rikicin majalisar da aka yi, domin sauran ‘yan majalisun 17 su ma sun je an rantsar da su a cikin majalisa ta tara,”

“Don haka, muna son mu jawo hankalin shugaban kasa Muhamamdu Buhari, da cewar jama’an jihar Bauchi ba su sha’awar jam’iyyar APC. Wannan ne ya haifar da shan kayen da jam’iyyar ta yi a zaben 2019, biyo bayan kauce wa matakan da suka dace a bi da zasu kai ga gina jam’iyyar a matakin jihar.

“Mambobin APC da daman gaske sun bayar da gagarumar gudunmawa wajen samun nasarar jam’iyyar PDP a jihar, sabili da gaza gudanar da demokradiyya a lokacin zaben fitar da gwani da jam’iyyar ta yi a zaben 2019 wanda hakan ya jawo asara da rugujewar abubuwa a karkashin tsohon gwamna Abubakar,” a fadin su.

Jawabin bayan taron, ya kuma shaida cewar tsohon gwamnan yayi aiki wajen yakar tsohon kakakin majalisar tarayya Yakubu Dogara da wasu mambobin APC da dama wadanda suka hada karfi wuri guda suka tabbatar da kayar da shi a jihar. 

“Muna kuma son mu fada wa shugaban kasa Buhari cewar, da gangan Muhammad Abubakar ya ki hada kan ‘ya’yan jam’iyyar APC a jihar a bisa son ransa da muradinsa na kashin kai ba na jam’iyyar ko na jiha ba. A bisa haka, tsohon gwamnan babu wani abun da zai iya nunawa na ribar demokradiyya da ya iya samar wa jama’an jihar Bauchi da ma Nijeriya gaba daya,”

A bisa haka ne kungiyar ‘yan takarar ta nemi shugaban kasa da ya daina sauraron mutanen da basu iya tsinana wa jihohinsu komai ba domin kauce wa bakin jini daga wajen jama’an da suka shaidi hakan.

A gefe guda kuma, kungiyar ta nemi shugaban jam’iyyar APC na kasa, Kwamared Adams Oshiomhole da yayi amfani da karfin ikonsa wajen hada kan ‘ya’yan jam’iyyar APC a jihar ta Bauchi domin kauce wa kubucewar shugabancin majalisar jihar a hanun APC, suna masu shaida masa cewar ‘yan APC ne ke kalubalantar shugabancin dan APC a bisa ra’ayinsu na kashin kai.

“Yanzu haka shugaban majalisar dokokin jihar Bauchi din nan Abubakar Y. Sulaiman dan APC ne, abun mamaki, wai ‘yan APC ne kuma ke kalubalantar nasarar shi. Dan PDP suke so ya zama Kakakin majalisar?

“Barista Muhammad Abubakar a bisa gazawar iya shugabancinsa ya sanya jama’a da dama suka yanke kauna da gwamnatinsa da kuma canza shi. Muna son mu tambayi Muhammad Abubakar cewar mene ne ya sanya ya dage ya cije sai Hon. Kawuwa Damina ya zama Kakakin majalisar jihar Bauchi? Alhali da kansa ya baiwa Abubakar Sulaiman tikicin takara a zaben da aka gudanar,” A fadinsu.

Jawabin ya kuma yi amfani da wannan damar wajen taya sabbin ministocin shugaban kasa Buhari a nes lebul, Adamu Adamu da Maryam Yalwaji Katagum da aka zaba daga Bauchi murna, da kuma musu addu’ar su rungumi kowa a jihar don tabbatar da jagoranci na kwarai.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!