Connect with us

WASANNI

Akwai Aiki A Gabana – Lampard

Published

on

Magoya bayan Chelsea sun fara maganar a kori kociyan kungiyar, Frank Lampard, bayan da kungiyar kwallon kafa ta Manchester United tayi laga-laga da Chelsea a wasan farko da kungiyar ta fafata a ranar Lahadin data gabata a filin wasa na Old Trafford.
Sai dai ba wannan ne karon farko ba a cikin makwannin da suka gabata da aka kaddamar da maudu’in neman a kori Lampard a Chelsea a shafin sadarwar na Twitter ba domin tun a watan daya gabata maganar ta fara yawo a Internet.
Tun a watan Yulin daya gabata aka fara kaddamar da maudu’in bayan wasan Lampard na farko a matsayin kocin Chelsea bayan ya gaza doke Bohemians ta kasar Ireland a wasan share fagen fara kakar wasa ta bana.
Wannan ne sakamako mafi muni a tarihin Chelsea a filin Old Trafford tun shekarar 1965 kuma sakamako mafi muni ga sabon koci a tarihin gasar firimiya tun Gustabo Poyet na Sunderland ya sha kashi 4-0 a Swansea a watan Oktoban 2013.
Kuma wannan ne karon farko da kociyan Chelsea ya sha kashi mafi muni a wasan shi na farko tun zamanin Danny Blanchflower da Middlesbrough ta doke 7-2 a 1978 sai dai Chelsea ta fi yawan taba kwallo a wasan, kuma ta fi kai harehare da daukar kwana.
Kuma Chelsea wadda aka haramtawa sayen ‘yan wasa, ta fara wasan ne da matasa kamar Mason Mount da Tammy Abraham da kuma Andreas Christensen duk da cewa Frank Lampard ya ce yana ganin bai kamata ace an doke Chelsea ba, amma ya ce wannan darasi ne inda ya amsa cewa Chelsea ta tafka kurakurai a wasan.
A ranar Laraba ne kuma Chelsea da ta lashe gasar Europa za ta hadu da Liberpool a wasan lashe gasar Super Cup na Turai a birnin Istanbul na kasar Turkiyya, kafin ta hadu da Leicester City a ranar Lahadi a gidanta dake Landan.
Wasu na ganin babban kalubalen da ke gaban Lampard, shi ne haduwar Chelsea da sauran manyan kungiyoyin Ingila kamar Manchester City da Liberpool da Arsenal da kuma kungiyar Tottenham.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: