Connect with us

Nahiyar Afirka

An Samu Nasarar Warkar Da Mutum Biyu Masu Cutar Ebola

Published

on

Hukumomin kiwon lafiya na Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kwango sun sanar da da cewa wasu mutum biyu da suka kamu da cutar Ebola sun warke gaba daya daga cutar, bayan gwajin sabon magani da aka yi musu.

Hukumomin kiwon lafiya a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kwango sun sanar da da cewa wasu mutane biyu da suka kamu da cutar Ebola sun warke sarai bayan da aka kwashe kwana 11 ana yi masu magani a birnin Goma na yankin gabashin kasar, wani abin da ke tabbatar da ingancin wasu sabbin magungunan yaki da cutar ta Ebola guda biyu da wasu Amurkawa suka samar.

Dama dai tun a ranar Litinin hukumomin kiwon lafiya na kasar Amurka wadanda suka dauki nauyin binciken samar da magungunan yaki da cutar ta Ebola sun sanar da cewa gwajin sabbin magungunan biyu da aka yi a wani asibitin kasar ta Kwango ya nunar da cewa adadin musu dauke da cutar ta Ebola da ke mutuwa bayan an yi gwajin kansu ya ja da baya da kaso 29 zuwa 34 cikin dari a yayin da kaso 60 zuwa 67 na wadanda ba su sha maganin ba ke mutuwa.

Alkaluman baya-bayan nan a kasar ta kwango sun sanar da cewa cutar ta Ebola ta hallaka ya zuwa yanzu kimanin mutum 1888 a kasar.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: