Connect with us

WASANNI

Har Yanzu Ba Mu Maye Gurbin Ronaldo Ba – Modric

Published

on

Dan wasan tsakiyar kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid kuma mai rike da kyautar gwarzon dan kwallo a duniya, Luka Modric, ya ce har yanzu, ‘yan wasan gaba na kungiyar sun kasa cike gibin da Cristiano Ronaldo ya bari.
Modric ya bayyana koken ne, bayan da kungiyarsa ta Real Madrid ta buga wasa da kungiyar kwallon kafa ta Roma a wani wasan sada zumunta sai dai yace nan gaba kadan zasu warware su cigaba da kokarinsu irin na shekarun baya. Gwarzon dan wasan ya ce tun bayan rabuwa da Cristiano Ronaldo da ya koma Jubentus, Real Madrid ta gaza ci gaba da nuna kwazo a wajen yawan zura kwallaye da kuma samun nasarori kamar yadda lamarin yake a baya.
Bayan rabuwa da Ronaldo, Real Madrid ta sayi ‘yan wasa masu kananan shekaru da suka hada da Binicius Junior da mariano Diaz, sai dai babu wani shahararren dan wasa da ta siyo domin maye gurbin da Ronaldo ya bari. A tsawon kusan shekaru 10 da Ronaldo ya shafe tare da Real Madrid, ya ci mata kwallaye 451, a wasanni 438 da ya buga mata. Sai dai bayan tafiyarsa Jubenus, kungiyar ta soma fuskantar matsaloli musamman wajen zura kwallo a raga.
A sati mai zuwa kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid zata fara buga wasan farko na laliga da kungiyar kwallon kafa ta Celta Vigo sai dai Modric yace yakamata wannan shekarar su lashe gasar laliga.
Real Madrid dai ta sayi manyan ‘yan wasa irinsu Edin Hazard daga Chelsea, wanda kungiyar ta bashi riga mai lamba bakwai kuma ake ganin zai maye gurbin Ronaldo, sai kuma Luca Jobic daga Frankfurt ta wasar Jamus da kuma Ferland Mendy daga Lyon sai kuma Rodrygo Goes da Militao
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: