Connect with us

TATTAUNAWA

Malama Mar’atus-Saliha Ta Yi Kira Ga Gwamnati Ta Dauki Mataki Kan Fyade

Published

on

MALAMA KHADIJA MUHAMMAD, wacce a ke yiwa lakabi da MAR’ATUSSALIHA, malama ce wacce ta shahara a kan ayyukan da su ka ta’allaka wajen bayar da tarbiyya ga matan aure da nuna mu su yadda a ke zamantakewar aure, nuna masu yanda ake tarbiyan yara, taimakawa marayu da zawarawa da makamantan hakan. Ta jima tana gudanar da wadannan ayyukan nata musamman a kasashen Nijeriya, Nijar da kuma kasar Togo. Ta tattauna da LEADERSHIP A YAU, a kan yanda take gudanar da ayyukan nata, da kuma irin matsalolin da take fuskanta, sannan ta bayar da shawarwari ga iyaye a kan tarbiyan yaran na su. Wakilin LEADERSHIP A YAU, UMAR A HUNKUYI, ne ya zanta da ita a gidanta da ke Kaduna. A sha karatu lafiya:

Sakacin Iyayen Yara: Ya kamata iyaye mata su ji tsoron Allah, domin ‘ya’yan nan da Allah Ya ba su amana ne, Ya ba su kiwo ne wanda zai tambaye su a ranar tashin kiyama. Ya kamata a ce mace ta killace ‘ya’yanta, ana so mace ta kasance mace wacce za a kira ta da sunan Mar’atus Saliha, (Mace tagari) wacce ita ce wacce take kula da amanar da Allah Ya ba ta, na kula da wadannan ‘ya’yan, za ta sanya ido wajen kula da fitansu da shigan su.

Yawanci matsalolin da ake samu sakaci ne na iyaye mata. Ana so mace ta sanya ido tun daga ‘ya’yanta a cikin gida, maza da mata, idan sun kai wani misali za a raba wuraren kwanciyar su. Yawan ado da kwalliya da ake yi wa yara ‘yan mata kananu yakan haddasa fasadin da ake yi wa yara fyade, yawan fita da nuna tsiraici da sanya tufafi kananu da ake yi yana sanya Zina ta yawaita a cikin al’umma.

Iyaye mata sune ya kamata su sanya ido a wajen tarbiyantar da ‘ya’yansu, matukar diyarki ta kai wani munzali kamar na shekara hudu da ake sake yara domin su ta fi Islamiyya ko boko, wannan ‘yar ya kamata duk wanda zai ta fi da ita ya kasance mai wayo ne. A nuna mata idan za ta fita ta yi addu’a, sannan in ta fita duk wanda ta gani da ba ta san shi ba ka da ta kula shi, idan ta dawo, uwa za ta tambaye ta, da wa, da wa kika hadu da shi, me ya faru, a nan diyar za ta saki jiki ta fada mata duk abin da yake faruwa.

Domin a mafi yawan lokuta wadannan abubuwan da ake fadawa a cikin su, iyaye sun bar wa malaman makaranta tarbiyar ‘ya’yan su ne su ba sa kiwon ‘ya’yan na su.

Kira Ga Gwamnati: Idan da ana daukan mataki da hukuntawa ga masu yi wa yara fyade, tabbas da wannan abin sam bai yawaita ba, hannu biyu su suka bayar da daman yin wadannan abubuwan, sakacin iyaye da kuma rashin daukan matakai da hukuntawa da ba a yi. Duk wanda ya aikata wannan laifin kamata ya yi a yi masa hukunci mai tsanani a kuma fito duniya a yada ta yanda idan wani ma zai yi zai san cewa lallai doka za ta dauki mataki a kansa. Ina kira ga gwamnati da ta taimaka wajen daukan mataki mai tsanani a kan masu aikata irin wannan barnan.

A kuma ja hankalin iyaye wajen killace ‘ya’yansu, yawan fa kwalliyar nan da ake yi ana fitowa kan tituna tana haddasa abubuwa da dama na barna. Da fatan Allah Ya kiyaye mana.

Yanda Na Ke Gudanar Da Da’awata: Nakan yi yawo ne gari-gari, a duk inda na isa wani gari nakan je na biya kudi na kama babban waje na shiga kafafen yada labarai na yi sanarwa, ni Mar’atus Saliha ina da taruka a Anguwa kaza, a waje kaza, inda idan na yi wannan kiran sai ka ga mata sun fito sosai.

Hikima ta a kan hakan shi ne, idan na shiga wani wajen na ce a tara mani mata nakan sami matsala, shi ne sai na ga gwamma na isar da da’awata ta hanyar kafafen yada labarai, in na shiga kafar yada labarai na biya, mata za su saurari dan tsokacin da zan yi kadan, don haka idan na ce ina da taro a waje kaza matan za su zo.

Farko nakan ja hankalinsu a kan Ikhalasi da takawa, wanda shi zai sanya rayuwar Duniya ta inganta, wanda kuma shi ne abin da ya yi karanci a halin yanzun, duk wani fasadi da kuke ganin ana aikatawa rashin tsoron Allah ne ya sanya ake samun wannan matsalar.

Yadda Na Ke Gyara Amare: A lokacin da nake zaune a wuri daya ne nake yin wannan aikin, a kan kawo wata yarinya ta yi har wata guda a wajena, wata makwanni uku,
wata makwanni biyu, wata ma fiye da hakanan din, tun da ni ina da gidan marayu ne na kaina, wanda na saya da kaina na kuma gina shi a kasar Togo.

Har yanzun a can din inda nake nakan gudanar da wannan aikin, za a kawo yarinya idan dai marainiya ce, ni zan dauki nauyinta komai da komai har ma a daura aure a gidana. Amma da na shigo nan Nijeriya na fara wannan aikin ba zaune nake a wuri guda ba, ina yawo ne gari-gari.

To ka ga in ce a kawo yarinya ta zauna a wurina ba zai yiwu ba sabili da ba a zaune ne nake ba. To ganin ba a zaune nake ba shi ya sanya idan na shigo gari nakan yi mai gaba-daya ne, da budurwar da za a yi wa aure da matan auren, a wannan zamantakewar zan nuna masu shi a aikace a cikin zaman da za mu yi da su, in ma a Masallaci ne zan yi da’awa zan yi shi gaba-daya ne, a kan Ikhlasi da tauhidi da kuma matsalolin da suka shafi mata, kamar matsalar ciwon sanyi da take hana mata rawar gaban hantsi, har su kansu ma mazan.

A kuma fito da duk matsalolin da suke a cikin rayuwar aure, a nuna ga yanda da namiji yake da bukatar a yi masa, a kuma nuna ga yanda mace ya kamata ta samu, in kuma ba ta samu ba ta yi hakuri saboda aljannah muke nema.

Ni Kadai Na Ke Yin Aikina: Yau shekara ta 18 ina wannan aikin ban taba samun taimako daga hannun wani ba, ko gwamnati ko al’ummar gari.

Taimakon shi ne idan na shigo na yi da’awa, a lokacin da nake son na sayi wancan gidan da nake son na saya na garin Togo, an sanya mani kudi milyan 15, sai na fito da kungiyar cewa mata su zo su sayi fom domin na rika koya yanda ake zamantakewar aure da sauransu.

Na sanya kudin fom din 2000, sai hassada ta shiga ciki, da na fahimci cewa wannan al’amarin zai janyo mani bakin jini a ga kamar ina tara mutane ne saboda in sami kudi, sai na janye.

Na roki Allah Ya kawo mani mafita, na je na yi karatu a kan matsalolin da suka shafi mata, na zama likita na Musulunci. A wannan likitancin da na koya nan nake samun kudi, saboda nakan hada magunguna a kan misali 2000 ko 3000, 5000 zan hada magani na, wannan kudin da nake samu a fannin magani na.

Da su na ke hidiman marayu na, da su nake yin komai. A haka ne kuma Allah Ya ba ni kudin da na sayi wannan wajen, a wancan lokacin ban ma yi rajista a kan ina da wata kungiya ba, amma yanzun da na yi rajista ina sanarwa ga duk wanda ya ga yana da bukatar taimakawa ko kuma ayyukan da nake yi sun birge shi yana da bukatar ya kawo tallafinsa kofa tana bude.

Tun daga gwamnati da masu hannu da shuni, in ba ku manta ba na nuna maku hotuna na irin ayyukan da nake shiga kauyuka ina yi, na kan dauki yarana mu shiga kauye mu kai masu kayan abinci, mu yi da’awa mu raba masu abubuwa mu dawo.

Duk a bangaren marayu da zawarawan da mazajen su suka mutu, duk wannan aikin ina yi ne daga aljihu na babu sisin wani a ciki. Sai dai yanzun da na kafa kungiya mukan ce mata su rika tara naira biyar-biyar, mukan kuma yi aiki da wannan biyar-biyar din da sukan tara, kamar a nan Rigasa, a watan Ramadan da ya gabata mun yi aiki, mun tara marayu 250 muka dinka masu kayan Sallah. Da yardan Allah kuma duk mun kakkafa irin wannan a Jihohin Bauci, Sakkwato da dai duk Jihohin da nake da mutane kafin dai wata gudummawar daga Ubangiji ta iso.

A Kan Kwalliyar Da Yara Mata Ke Yi Ranar Yawon Sallah: A gaskiya ya kamata iyaye su ji tsoron Allah, tun daga ranar Idi, kwalliya da za a yi a fita, Musuluncin mu fa ya nuna mana komai muna da ka’ida. Yawon idi zumunci ne, amma a yi shi a bisa yanda zai bayar da fa’ida, kar a saki yara su kadai su ta fi suna roko a koya masu bara, a killace yaran, idan an tashi fita sai a sami abin hawa wanda za a dauki yaran da iyayensu a je a yi ziyarar wacce take ya kamata a yi ta.

In kuma an je ziyarar a nuna wa yaran ko an ba su abu su zama masu kunya ba kamar yanda za ka ga wasu yaran har sanya hannu suke yi a cikin aljihu su ce ba ni barka
da Sallah ba. Ina kira ga iyaye su koya wa yaran su tarbiya su hana su roko, kamata ya yi su iyayen su amfanar da ‘ya’yan na su da abin da zai hana su yin roko, ya kamata a ranar Sallah mahaifi ya fito ya canza misali naira hamsin biyar-biyar sai ya rabawa ‘ya’yan nan na shi kanana za su ji dadi ba sai sun je sun roki wani ba.

Amma a bar yara su fita suna yawo har dare, suna shan wahala suna watangaririya wasu ma su bata, daga nan ne kuma ake bata tarbiyar yara, domin sau da dama a wannan lokacin ne ‘yan mata suke samun lokaci su je su yi badala da samari, har a fitar da ‘yarki ba ki sani ba saboda kin ce ta je gidan wane ba tare da muharraminta namiji ba wanda ya san haramci ya san halasci.

Zuwan Yara Wuraren Shakatawa: Duk wurin da ba wurin Allah ne ba, bai kamata a je shi ba, irin wuraren badala sam bai halasta a je su ba, duk wurin da yake akwai sabon Allah, kide-kide, raye-raye, fasikanci, fajiranci haramun ne ku bar ‘ya’yanku su je can. Akwai wuraren da ya dace a Musulunci a je, yau in an ce Sallah ce, akwai wuraren da za a je da uwa da uba da ‘ya’yan a yi abinci a je a zauna a yi nishadi a ci a sha. Yana da kyau iyaye su rika zuwa wadannan wuraren da su da ‘ya’yansu su zauna a can domin nishadin su. In ma ‘life’ ne kamar yanda ake cewa da Turanci, su yi badala da samari, har a fitar da ‘yarki ba ki sani ba saboda kin ce ta je gidan wane ba tare da muharraminta namiji ba wanda ya san haramci ya san halasci.

Zuwan Yara Wuraren Shakatawa: Duk wurin da ba wurin Allah ne ba, bai kamata a je shi ba, irin wuraren badala sam bai halasta a je su ba, duk wurin da yake akwai sabon Allah, kide-kide, raye-raye, fasikanci, fajiranci haramun ne ku bar ‘ya’yanku su je can. Akwai wuraren da ya dace a Musulunci a je, yau in an ce Sallah ce, akwai wuraren da za a je da uwa da uba da ‘ya’yan a yi abinci a je a zauna a yi nishadi a ci a sha.

Yana da kyau iyaye su rika zuwa wadannan wuraren da su da ‘ya’yansu su zauna a can domin nishadin su. In ma ‘life’ ne kamar yanda ake cewa da Turanci, su Turawan ma in sun tashi ba da ‘ya’yansu suke zuwa ba? ai ba sake su suke hakanan kawai kara zube ba, shari’ar Musulunci ba ta yarda da wannan ba.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: