Connect with us

RIGAR 'YANCI

Muna Son Gwamnan Kano Ya Tuna Da Kungiyoyin Mata – Zainab Musa

Published

on

HAJIYA ZAINAB ALI MUSA dai ba bakuwa ba ce wajen shiga kafafan yada labarai na rediyo da sauran jaridu, don fayyace al’amuran da suka shafi harkokin mata. Kazalika, ita ce Shugabar Kugiyar mata ta National Birac society a Jihar Kano. Wakilin LEADERSHIP A YAU, HARUNA AKARADA, ya samu zantawa da ita. Ga yadda tattaunawar ta kasance:
Hajiya ga shi yanzu an kammala zabe kuma mata sun ba da gudunmawa wajen kafa wannan Gwamnati, sannan kin ta kirayekiraye wajen baiwa wadannan mata dama domin su ma a dama da su, me za ki ce game da wannan yanzu?

To, ai ba za mu idar wannan kiraye-kiraye ba, har sai an kammala wa’adin wannan mulki mun gani ko Mai girma Gwamna zai cika mana alkawarurrukan day a dauka. Sannan ita kanta Uwargidansa, ta yi alkawarin cewa za ta taimaka wa mata, sakamakon irin gudunmawar da suka bayar ta fuskar jajircewa da suka yi suka fito suka yi zabe, musamman zaben da aka yi a Unguwar Gama, don kusan tarewa muka je muka yi a wannan Unguwa har sai da muka tabbatar an ci zaben nan tukunna sannan muka koma gidajenmu.

Sha’anin mata, wani abu ne da suke neman tallafi a Gwamnati a koda yaushe, kina ganin wannan sabuwar Gwamnati za ta kula da ku mata kuwa?

To a nan babu abin da zan ce, illa muna yi wa Gwamna tini, dalili kuwa akwai mata da dama da kuma sauran ‘ya’yan kungiyarmu wadanda suka sha wahala matuka da gaske. Saboda haka, a halin yanzu so muke yi Mai girma Gwamna, ya kalli irin wannan wahala da mata suka sha, ba za mu ce bai yi komai ba, amma dai a wannan sabuwar Gwamnatin ma, mata ya kyautu su amfana a wajen rabon Kwamashinoni, a jawo su ciki, sannan a tabbata an nemo ‘yan siyasa wadanda suka san mutincin dan siyasa.

Haka zalika, a rika kokarin zakulo ‘yan siyasa wadanda aka sha wahala tare da su, ba lallai sai wadanda suka kashe kudi ba, a’a akwai wadanda suka fito tsakani da Allah suka taimaki Gwamnati, to irin su duk wanda Gwamna ta baiwa irin wadannan kujeru za su iya rike jama’a.

Har ila yau, wajibi ne a yi hankali da ‘yan shan kai, domin kuwa sai an gama wahala kaf sai wasu su tsallako su ci moriyar abin, sannan sai ku kuma a jefar da ku gefe guda. Amma idan aka baiwa mata, ko shakka babu mun san cewa mace ko babu komai, akwai ta da tausayi, sannan kuma za su yi bakin kokarinsu.

Haka nan, ya kamata Uwargidan Gwamna ta shige mana gaba mu mata mu samu gwababan mukamai, sannan idan an samu, kirana ga matan shi ne su yi kokari su fidda ita kunya, sannan wajibi ne mu ma mu yi alfahari da ita cewa, ai matar Gwamna ce ta taimaka mana mu mata.

Duk da wannan maganar da kika yi na lura cewa, irin ku tunda kuke bin wannan Gwamnati ba ku taba yin rawa ba, ko wani salo na ‘yan siyasa kina ganin wannan karon za a faranta muku rai?

To gaskiya ni Shugabar Kungiya ce a wannan Jihar ta Kano, sannan da ma ita wannan kungiya Gwamnati ce ke daukar nauyinta, don haka a namu bangaran, mun yi iya namu, kasan a wannan kungiyar tamu, an taba samun Minista, wato Zainab Maina, ‘yar wannan kungiyar ce, sannan ga Hjjiya Hajjo, ita ma ta Fadar Shugaban Kasa ce, sannan kuma ita ma ‘yar wannan kungiyar ce, ko wannan rantsar da Shugaban Kasar ma da aka yi wakilan wannan kungiya tamu na wannan wuri.

A ina da ina wannan kungiya taku ke da Ofisoshi?

Mu na da Ofisoshi a dukkanin Kananan Hukumomi 44 da ke wannan Jiha, sannan idan lokacin zabe ya zo muna zuwa mu yi zabe.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: