Connect with us

LABARAI

Tsaro: Kwamishinan ‘Yan Sandan Neja Ya Nemi Jama’a Su Taimaka Wa Kudurinsu

Published

on

Kwamishinan rundunar ‘yan sandar Neja, Alhaji Usman Adamu ya bukaci shugabannin al’umma da su taimakawa rundunarsa na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar. Kwamishinan ya bayyana hakan ne a tabakin Wakilin sa, mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, DCP Godwin Eze a taron bada tallafin Keke-Napep ga kungiyar ‘yan sintirin unguwar Barikin Sale da gidauniyar Garkuwan Talban minna ta bayar lahadin makon jiya a harabar ofishin ‘yan sintirin da ke unguwar Barikin Sale a karamar hukumar Chanchaga.

Tunda farko kwamishinan ya yaba da irin wannan kwazon na wannan gidauniyar, da za a samu shugabannin al’umma da masu hannu da shuni za su rika yin irin wannan hubbasar na tsaron unguwanninsu da jami’an ‘yan sanda sun samu saukin tafiyar da ayyuka yadda ya kamata, ya kamata kowace unguwa ta samar da kwamitin da zai rika sanya ido akan batagari ta hanyar hadin kai da jami’an tsaro duk wanda suka ga zai zama barazana ga zaman lafiya a tabbatar an sanar da jami’an ‘yan sanda dan daukar matakin gaggawa ta hanyar dakile batagari da ke fakewa a cikin al’umma, hakan zai sa a samu sassauci wajen zamantakewar al’umma.

Da ya ke bayani a taron, shugaban gidauniyar Garkuwan Talban Minna, Alhaji Sulaiman Yahaya Babangida, Cikasoron Minna, Gado Da Masun Bargu kuma Barde Kerarriyar Agaie, yace tun da farko gidauniyarsa ta baiwa marasa karfi tallafin abincin sallah da kudade su a kallan mutum dari biyar dan samun saukin gudanar da bukukuwan sallah.

Dangane da halin da matasan unguwar Barikin Sale kuwa, yanzu-yanzu haka gidauniyarsa ta dauki nauyin matasa uku a cikin unguwar wadanda ke karatun difloma a mataki daban-daban, wanda kuma lokaci-lokaci zasu cigaba da yin wannan. Haka kuma yace ya umurci kwamitin tsaro na unguwar da samu wata cibiyar da za a rika horar da matasa sana’o’in hannu, a shirye yake wajen daukar nauyin cibiyar.

Ya ce dalilin bada wannan Keke-Napep da kungiyar sintirin Barikin Sale, mun ga irin kwazon da su ke yi wajen sanya idanu akan yadda harkokin matasa ke gudana a cikin unguwar nan, duba da halin da ake ciki kuma ba su da hanyar samun kudin shiga balle su iya biyan kansu alawus na wata-wata, mun baiwa wannan kungiyar KekeNapep dan samun kudin shiga da zai baiwa kungiyar damar samun kudin shiga da za ta iya daukar nauyin wasu lalurorinta ba tare da wdogaro da mutane ba.

An yi gwamnatoci da dama a jihar Neja kuma kowa ya taka rawarsa wajen gina wannan unguwa, amma tun hawar gwamna Abubakar Sani Bello ba wani abin azo a gani da ya kawo wa al’ummar wannan unguwar duk da cewar muna daga cikin unguwannin da suka ba shi kuri’a a lokacin zaben sa na farko da na biyu da ya gudana.

Don haka mu na jawo hankalin gwamna, da ya kokarta kamar yadda gwamnatocin baya suka yi na samar da wasu abubuwan cigaban a kasa a unguwar nan da shi ma yayi kokarin barin wani abu da jama’ar Barikin Sale za su a lokacinsa aka samar da su na alheri.

Barikin Sale mu na da matsaloli da dama, kuma muna bukatar daukin gwamnati, duk da cewar tsohon shugaban karamar hukumar Chanchaga, Hon. Yusuf Inuwa Fuka ya taka rawar gani, ba mu taba samun shugaban karamar hukumar Chanchaga da ya taba rayuwar matasan mu ba, kamar yadda ya yi ba.

Domin ya dauki dawainiyar karatun matasa talatin da uku wanda Barikin Sale kawai ta samu gurbin mutum biyu, bayan wasu ayyukan cigaban kasa da ya gudanar a wannan unguwar lokacin mulkinsa. Da ya juya kan kungiyar ‘yan sintirin kuwa, yace su ji tsoron Allah su sani wannan aikin amana ce aka ba su, dan haka kar su yi anfani da wannan damar su na cin zarafin jama’a.

Ina kira ga kwamitin tsaro na wannan unguwa da su rika zama lokaci-lokaci dan bibiyar yadda ayyukan tsaron ke gudana, sannan dattijai da matasa da masu unguwanni da su bai wa wannan kungiyar hadin kai dan samun cigaban Barikin Sale.

Da ya ke karin haske ga manema labarai, shugaban kwamitin tsaro na unguwar Barikin Sale, Kwamared Abdullahi Jabi, ya ce, lallai bayan kafa wannan kwamitin sintiri, sun fuskanci matsaloli a tafiyar, domin watanni takwas ke nan ba su iya biyan alawus na wata ba ga jami’an sintirin amma duk da haka ba su yi kasa a guiwa ba, zamu tabbatar da irin wannan tallafin da muke samu daga hannun manyan unguwa mun tsare mutuncin ‘yan sintirin mu.

Yanzu haka mun samu gayyata daga wata kungiyar horar da ‘yan sintiri a garin Abuja, kuma tsohon shugaban karamar hukumar Chanchaga, Hon. Yusuf Inuwa Fuka ( Scony) ya yi alkawalin daukar nauyin mutum biyar, kuma damar mutum goma aka ba mu damar kaiwa, za mu yi kokarin lokacin dan ganin mun cika gurbin mutane goman nan, yanzu dai ka ga mun samu ofis a nan cikin unguwa, kuma mun samu hadin kan jami’an tsaro na ‘yan sanda, yanzu kuma ga tallafin Keke-Napep mun samu, abinda ya rage mana shi ne samar masu yunifom, takalmi da hula gami da takalmi, kuma shi ma ba zamu dau lokaci ba zamu samar da su.

Daga cikin wadanda su ka halarci bukin sun hada da kwamishinan ‘yan sandan jiha, bisa wakilcin mataimakin sa, DCP Godwin Eze, sai mai unguwar Barikin Sale, Alhaji Dogo Sulaiman, da tsohon shugaban karamar hukumar Chanchaga, Hon. Yusuf Inuwa Fuka. Sauran sun hada da babban daraktan hukumar NOMADIC, Alhaji Adamu Babayo da shugaban taron Alhaji Sulaiman Yahaya Babangida, da sauran jami’an tsaron farin kaya da goyon bayan kungiyar matasan ‘yan Kasuwan minna ( Young Marketers Association) bisa jagorancin shugabanta, Alhaji Isyaku Sani Dokto.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: