Connect with us

KASASHEN WAJE

Amurka Ta Tsaurara Matakan Ba Da Izinin Zama Kasar

Published

on

A ranar Litinin Gwamnatin Trump ta yi shelar bullo da wani tsari, wanda zai hana bakin hauren da ke cikin Kasar samun takardar zama dindindin ko ta zama dan Kasa, muddun sun dogara ne ga taimakon gwamnati, irin na kiwon lafiya, da abinci ko kuma muhalli.

Ken Cuccinelli, mukaddashin Shugaban hukumar shigi da fici da kuma bayar da takardar shaidar zama dan Kasa, ya yi shelar abin da ya kira, “Tsarin Hana Shigowa Amurka Don a Dogara ga Tallafin Gwamnati,” wanda, a ta bakinsa, “ Zai karfafa gwiwar masu niyyar shigowa, ko ci gaba da zama Amurka, su yi shirin tashi su nemi na kansu, su kuma zama masu dogaro da kai.”

Sabon tsarin zai fara aiki ne ranar 15 ga watan Oktoba na shekarar 2019. A karkashin tsarin, an fassara wanda ya zama nawaya ga gwamnati da wanda ya amfana da wani, ko wasu tallafi na gwamnati na tsawon watanni sama da 12 a tsawon watanni 36. A karkashin wannan tsarin, za a kirga karbar tallafi sau biyu a wata guda a matsayin watanni biyu. A wani rahoton mai kama da wannan kuma, Shugaban Amurka Donald Trump, ya sanar da shirin kafa dokokin da za su haramta bai wa bakin-hauren samun takardun izinin zama na din-din-din da kuma na shaidar zama ‘yan Kasa.

Shirin na gwamnatin Amurka babban koma baya ne ga fatan zama ‘yan Kasa da miliyoyin bakin-hauren da ke gudanar da wasu kananan ayyuka a Kasar ke da shi.

Kazalika, shirin zai kuma rufewa bakin-hauren kofofin samun damar shiga Amurka domin amfana da kananan guraben ayyuka, da sauran ababen more rayuwa da suka hada da lafiya da kuma ilimi.

Sabuwar dokar da Shugaba Trump ke shirin kafawa za ta shafi akalla bakin-haure miliyan 22 masu kananan ayyuka dake da takardun izinin zama a Kasar, da kuma wasu karin ‘yan ci ranin miliyan 10 da rabi da suka dade zaune a Amurka ba tare da izini ba.

Cikin watan Mayun da ya gabata Shugaban Amurka Donald Trump ya ce Kasar na bukatar tarin baki-haure, amma wadanda suka kware akan sana’o’i daban-daban.

Trump ya bayyana haka ne yayin gabatar da sabon shirin gwamnatinsa dangane da karbar baki.

Shugaban ya ce sabon shirin zai ba da damar kara yawan irin wadannan baki kwararru daga kashi 12 zuwa kashi 57 ko fiye da haka, domin ganin Amurka ta tsaya daidai da sauran kasashen duniya.

Trump ya kara da cewa Amurka na alfahari da bude kofar da za ta yi, amma dole wadanda za su amfana da wannan shirin ya kasance kwararru ne wadanda kuma suka iya Turancin Ingilishi da za su zana jarabawa kafin samun damar.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: