Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

An Kashe Shugaban Mafarauta Da Dansa A Kogi

Published

on

An kashe shugaban mafarauta na karamar hukumar Kabba da Bunu, ta Jihar Kogi, Caleb Oshe, tare da dansa.

A ranar Lahadi ce aka bayar da labarin kisan na Oshe da dan na shi, wanda wasu ‘yan bindiga suka yi da jijjifin safiyar ranar Talata.

Gwamnatin Jihar ta Kogi ta yi tir da kisan, tana mai cewa, za a kama wadanda suka aikata kisan domin su fuskanci hukunci.

Cikin wata sanarwa ta hannun babban daraktan yada labarai na Gwamnan Jihar, Kingsley Fanwo, tana cewa, Gwamnan Jihar Yahaya Bello, ya kwatanta kisan da cewa ba abar amincewa ce ba.

Ya yi kira da a kwantar da hankali, yana mai cewa, ìShakka babu, an aike da hukumomin tsaro domin su tabbatar da sun damko makasan.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!