Connect with us

LABARAI

Babbar Sallah 2019: Coci Ta Raba Barka Da Sallah A Kaduna

Published

on

Sanannen Fasto a jihar Kaduna, Yohanna Buru, a karkashin cocin da ya ke jagoranta mai suna Christ Ebangelical and Life Intercessory Fellowship Ministry da ke a unguwar Sabon Tasha cikin garin Kaduna ta yi rabon barka da sallah na kayan abinci ga nakasassu da ’yan gudun hijira sama da 200.
Yohanna Buru, a hirarsa da manema labarai jin kadan bayan rabar da kayan abincin, ya ce, an rabar da kayan ne don kara dankon zumunci da kuma kara wanzar da zaman lafiya a jihar, musamman a tsakanin mabiya addinin Kirista da na Musulunci.
Ya kara da cewa an kuma yi hakan ne da nufin tallafa wa rayuwar marasa karfi da ke cikin jihar, musamman nakasassu, almajirai da kuma ’yan gudun hijhira yadda su ma za su san cewa ba a manta da su ba.
Fasto Buru ya ce, “ba wai yau mu ka fara irin wannan tallafin ba, domin mun shafe shekaru mu na yin hakan, musamman a lokacin gudanar da shagulgulan sallah da kuma lokacin gudanar da yin azumin watan Ramadan.”
A cewarsa, a shekarar da ta gabata, sama da abinci 1,100 Cocin ta raba wa marasa karfi da ke cikin jihar Kaduna da su ka hada da ’yan gudun hijira, nakasassu, almajirai da kuma masu zaman gidan kaso a jihar a lokacin azumin watan Ramadan na bana, inda ya ce, cocin ta yi hakan ne don ta dadada mu su rai. Buru ya yi nuni da cewa, daukacin Musulmai da Kiristoci duk jikokin Annabi Adam da Hauwa’u ne kuma dukkan Musulmai da Kiritoci Allah su ke bautawa.
Ya koka a kan yadda karin farashin kayan masarufi ya ke jefa rayuwar al’umma, musamman talakawa, a cikin ukubar rayuwa. Buru ya kuma yi kira ga daukacin Musumai da ke a daukacin fadin Najeriya, da matakan gwamnati uku da ke a kasar, da su rungumi dabi’ar taimaka wa marasa galihu, musamman da dan abin da za su ci.
Da ya ke karbar tallafin na kayan abinci a madadin sauran da su ka amfana a gidan nakasassu da ke kan Titin Kano a birnin Kaduna, Mallam Tukur Zubairu, wanda kuma shi ne Shugaban Makafi na jihar, ya godewa Fasto Buru da talafin, inda ya shawarci faston da kada ya gajiya a kan taimakon, domin Allah ne zai iya biyan sa.
Mallam Tukar ya tabbatar da cewa, duk shekara Fasto Buru ya na kawo mu su irin wannan tallafin har da lokacin gudanar da Azumin watan Ramada, Shi ma a nasa jawabin, Shugaban Cibiyar Killace masu Shaye-shaye da kuma tabin hankali, Mallam Lawal Maduru, wanda a ka fi sani da Malam Niggas, ya yi kira ga daukacin Musulmai masu hannu da shuni su yi koyi da Fasto Buru wajen taimaka wa marasa karfi.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: