Connect with us

LABARAI

Hawan Sallah: Hakimai 11 A Kano Sun Yi Watsi Da Umarnin Ganduje

Published

on

Wasu Hakimai 11 a jihar Kano sun bijire wa umarnin Gwamnatin Jihar, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, bisa umartar su da su tsaya a yankunan masarautunsu domin gudanar da Hawan Daushe da kuma sauran Hawan Sallah tare da sarakunansu masu daraja ta xaya.

Waxannan Hakimai dai su ne waxanda su ka faxa yankunan sabbin masarautun da gwamnan jihar ta Kano ya qirqira, inda su ka halarci Hawan Daushe na yammacin ranar Litinin a Masarautar Sarkin Kano ta Mai Martaba Muhammadu Sanusi II.

Idan a na biye da mu, za a iya tunawa da cewa, tuni dai Gwamnatin Jihar Kano ta fitar da sanarwa cewa, kowane hakimi ya zauna a yankin masarautarsa, don gudanar da Hawan Daushe, wanda a ka saba yi bisa al’ada a duk ranar xaya ga sallah. Amma sai ga shi wasu daga cikin Hakiman 11, sun bijire wa wannan umarni na Gwamnatin Jihar ta Kano, sun tafi Masarautar da ba tasu ba don gudanar da bikin wannan Hawa na Daushe.

Hakiman da su ka kauracewa wannan umarni na Gwamnatin Kano, tare da yin biyayya ga Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, sun hada da Madakin Kano; Yusuf Nabahani (Hakimin Dawakin Tofa), Dan Amar Aliyu Harazimi Umar (Hakimin Karamar Hukumar Doguwa), Muhammad Aliyu (Hakimin Garko), Makama; Sarki Ibrahim (Hakimin Wudil), Sarkin Fulanin Ja’idinawa Buhari Muhammad (Hakimin Karamar Hukumar Garun Malam, da kuma Barde; Idris Bayero (Hakimin Karamar Hukumar Bichi).

Sauran sun hada da: Sarkin Bai; Alhaji Adnan Mukhtar (Hakimin Karamar Hukumar Danbatta), Yarima Lamido Abubakar (Hakimin Karamar Hukumar Takai), Dan Isa; Kabiru Hashim (Hakimin Warawa), Dan Madami; Hamza Bayero (Hakimin Karamar Hukumar Kiru) da kuma Sarkin Dawaki Mai Tuta; Bello Abubakar (Hakimin Karamar Hukumar Gabasawa).

Har ila yau, a wata sanarwa da  Kakakin Gwamnan Jihar Kano, Abba Anwar ya fitar a ranar Lahadin da ta gabata, Gwamnatin Kano, ta bukaci daukacin Hakimai da su yi watsi da umarnin

Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi 11, na zuwa birnin Kano domin gudanar da Hawan Sallah tare da umartar su, da gudanar da Hawan Daushe karkashin sabbin Masarautunsu.

Umarnin Gwamnatin Jihar, kwata-kwata ya yi hannun riga da sanarwar da Fadar Masarautar Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ta fitar, inda ta gayyaci dukkanin Hakiman Jihar Kano, domin halartar Hawan Daushe, wanda aka saba yi a dukkanin ranar daya ga Sallah.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: