Connect with us

KIWON LAFIYA

NCDC Ta Bayyana Barkewar Cutar Shawara A Ebonyi

Published

on

Hukumar hana yaduwar cututtuka da kuma maganin su ta kasa ta bayyana cewar tana da masaniya dangane da barkewar ita annobar cutar zazzabin shawara a   Ebonyi. Cibiyar ta bayyana hakan ne a wata sanarwar da Shugabanta  Chikwe Ihekweazu, ya sa ma hannu wadda kuma aka bayyanawa manema labarai ranar Asabar ta makon daya gabata. NCDC ta bayyana cewar ‘yan tawagarta na kota baci, tuni suka riga suka je can jihar tun 30 ga watan Yuli, na wannan shekarar, tare  kuma da hadin kan Hukumar lafiya ta duniya.

“Bayanan da suka biyo bayan barkewar ita cutar da kuma mace- macen da aka samu sanadiyar hakan, saboda kuma ba a san ma daga inda shi al’amarin cutar ta zazzabin ya bullo ba. a karamar Hukmar Izzi, a jihar ta Ebonyi. Tawagar kula da lafiyar al’umma ta jihar sai kawai ta fara yin bincike, kuma ya zuwa da 31 ga watan Yuli na wannan shekarar da muke ciki, indea kuma aka samu mutane uku bayan an yi bincike ka gano sun kamu da shi zazzabin na shawara. Shi kuma gwajin an yi shine a dakin gwaji na Hukumar, wanda kuma hakan  ya sa aka samu damar kai taimako cikin sauri.

“Tawagar kwararru wanda su ne ya dace su dauki matakin daya daya dace dangane da wata cuta,m ita ce wadda ta shugabbanci tawagar wadanda suka kai taimnako, akan ita cutar ta zazzabin shawara tare da taimakonHukumar ta NCDC, sai kuma Hukumar kula da lafiya matakin farko  ta kasa, sai kuma Hukumar lafiya ta duniya.

“A cikin shi binciken da aka gudanar an gano cewar tsakanin 1 ga watan Mayu da kuma 7 ga watan Agusta na wannan shekarar, an samu labarin barkewar ita cutar ta zazzabin shawara, wadda har ma tayi sanadiyar mutuwar 20 a karamar Hukumar ta Izzi  a jihar Ebonyi. Wannan kuma shi ya nuna  afili cewar ita cutar ta dade tana yin barna watanni da suka wuce, wanda kuma ita Hukumar ta kulawa lafiyar al’umma ta karamar Hukumar ta kasa gane al’amarin da yake tafiya danagane da ita cutar.

Abin an riga an makaro har ma a ce za a dauki jinin  wadanda ake sa ran sun kamau da cutar don a gane gaskiyar al’amarin. “Tun da dai ta samu labarin yadda ko kuma irin halin da ake ciki danagane da shi al’amarin na cutar zazzabin na shawara, sai ita Hukumar ta aika da ‘yan tawagarta ba tare da bata lokaci ba, zuwa jihar ta Ebonyi domin su taimaka.  Wannan kuma abin ya shafi ko kuma ya hada da yadda za a gano inda shi al’amarin yake, da kuma wadanda ya shafa, yadda shi al’amarin na sadarwa zai iya taiumakawa, sai kuma yadda za a shawo kan ita cutar.

Ga dai yadda su al’amuran suke sai kuma tsarin wanda aka yi wanda kuam an riga an yi nisa, wani mataki wanda kuma babba ne, wanda kuma har ila yau ya kunshi yadda za a nemi damar ko kuma taimakon kasa da kasa akan alluran rigakafin da suka dace, ba domin komai ba, sai saboda a samu damar gamawa da ita ciutar kamara dai dai yadda bayanin ya nuna”.

Zazzabin shawara: Ita kwayar zazzabin shawara tana yaduwa ne ta hanyar cizon sauro wanda shi kuma yana dauke ne da su kwayoyin cutar, Zuwa yanzu dai ba a samu damar ganowa ba yadda shi mutum zai iya yada ita cutar. Saboda ita cutar ta shawara ana iya maganinta da yin allurai, idan kuma aka yi ma mutum ita tana iya taimaka ma shi da wata kariya, a duk tsawon rayuwar shi, kamar dai yadda ita Hukumar ta bayyana.

“Ita allurar ta zazzabin shawarar ana yenta kuma kyauta ce a kanana da kuma manaya asibitoci a Nijeriya,wanann kuma yana daga cikin irin alluran rigakafin da aka saba yi yau da kullun. Ana iya samun damar kare yaro har tsawon rayuwar shi, amma fa sai an yi mashi allurar rigakafin, Muna karffa ma dukkan iyalai su yi kokarin yin ita wannan allurar, domin su tabbatar da cewar an samu yi ma ‘ya’yan nasu allurar.

“Bugu da kari kuma ita allurar an ba mutane shawarar cewar su kula da tsaftace muhallin su, dukl kuma wasu wuraren da suka ganin ruwa yana tsayawa, su yi magani shi wajen, yin duk abinda zai sa ya rika wucewa. Yin hakan kuma zai han sauro su bar samun yanayi mai kyau wanda zai taimaka masu hayaiyafa. Bayannan kuma su rika yin amfani da maganin kwari saboda kashe su saurayen, ga kuma maganar kwana cikin gidan sauro wanda aka sa ma magani. Shi kuma maganin kwarin ana fesa shi ne har akan kofofi da kuma tagogi,saboda  ahana saun damar da sauro yake yi wajen cizon mutane.b Yana kuma da kyau ya bar tunani yi ma kan shi magani, amma kuma ya kamata ya je  asibiti da zarar ya ji baya jin dadin jikin shi.

“Tun watan Satumba na shekarar 2017 kasar Nijeriya ta samu wani mutum daya wanda ya kamu da zazzabin na shawara,a dukkanin jihohi na kasar, saboda kuw aya zuwa ranar 31 ga watan Yuni na shekarar 2019 aka samu mutane 78 sun kamau da ita cutar, wannan kuma ya biyo bayan da aka gwada su, a shekarar 2019 kadai. Sai dai kuma da akwai wata kungiya wadda ake kira da suna multi-agency Yellow fever, wadda ita kuma tana bayar da taimako ne na bangaren fasaha, wanda kuma ita Hukumar ta NCDC, take jagorancin ta wajen bincike – bincike, inda kuma hakan ya sa aka samo wadanda suka kamu da cutar suka ragu.

Ita kuma Hukumar kula da lafiya matakin farko ta kasa, ita ma tana wani jagoranci saboda kuwa ta bayar da wata dama ta samun wata allurar rigakafin, wannan kuma ta hanyar allurai na rigakafi wadanda kuma za su cutar ba a kamuwa da ita, amma kuma ta hanyar wayar da kan al’umma. “Su ma ma’aikatan kula da lafiya matakin farko ana kara tuna masu cewar su lura da alamunda ake gani tare da wanda ya kamu da ita cutar ta shawara, wadanda kuma suka hada da yadda idanu zasu kasance sunzama kamara ruwan dorowa, sai kuma zazzabi, ciwon kai, da kuma ciwon jiki,, idan mutum yana da wadannan abubuwa tare da shi, sai ya yi saurin garzayawa zuwa a sibiti domin ya ga Likita, wannan kuma  a asibiti mafi kusa da shi.”

Hukumar ko kuma cibiyar ta NCDC an kjafa ta ne a  shekarar 2011, wannan kuma saboda matakin da za a dauka , saboda kai martini saboda matsalolin dsa suka shafi kula da lafiyar al’umma, wadanda kuma suka kasance  na gaggawa, wannan kuma domin a nuna ai da gasker ne ake dangane da duk wasu matsalolin da za su iya tasowa, domin kawo karshensu. Musamman ma cututtukan da suke saurin yaduwa.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: