Connect with us

RIGAR 'YANCI

NULGE Za Ta Hana Gwamnoni Taba Kudaden Kananan Hukumomi – Kwamred Lapene

Published

on

An bayyana cewar kungiyar ma’aikatan kananan hukumomi tana zama dan tantance tsarin mafi karancin albashin ma’aikatan kananan hukumomi na naira dubu talatin ga mafi karancin albashi. Shugaban kungiyar ma’aikatan kananan hukumomi ( NULGE) reshen jihar Neja, Kwamared Idris Abdulkareem Lapene ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai kan mafi karancin albashin ma’aikata a minna fadar gwamnatin Neja.

Lapene yace akwai ma’aikatan da albashin su yafi karfin wannan tsarin dole sai an zauna an tantance kafin ya fara aiki, wanda yanzu haka muna kan tuntubar hukumomin da abin ya shafa dan yin nazari daidai da yadda dokokin kasa ya tanadar kan albashin ma’aikata. Da ya juya kan kudaden kananan hukumomi da ake zargin gwamnatocin jahohi na dan newa kuwa, yace sama da shekaru hudu muke ta yekuwar gwamnatocin jahohi su sakar wa kananan hukumomi mara ta yadda zasu samu damar gudanar da ayyuka a bangarorin kananan hukumomin su, domin mutanen da ke matakin kasa da yankunan karkaru ba sa samun damar samun abubuwan more rayuwa da ya ta’allaka ga shugabannin kananan hukumomi su samar masu.

Ya ce a matakin kungiyar ma’aikata muna sanya idanu akan yadda ake gudanar da mulki, a satin da ya gabata mun hadu da NFIU mun kuma sanar masu cewar abinda yake faruwa ba shi ne tsarin da aka yi na baiwa kananan hukumomi kudaden su ba, domin gwamnati na baiwa kananan hukumomi kudaden su da hannun dama suna karbewa da hannun hagu, kuma ita NFIU sun yi alkawalin bada sabon tsari kuma zai tafi kai tsaye ga bankuna, yadda su kuma zasu bi tsarin tafiyar da kananan hukumomi.

Aikin zai tafi ne kai tsaye zuwa kungiyar mu, domin mu zamu sanya ido mu ga yadda kananan hukumomin za su karbi kudaden da yadda zasu kashe su, wanda da zaran an dawo hutun sallah za mu baiwa dukkanin kananan hukumomi wannan sabon tsari kuma za mu tabbatar mun sanya idanu mu ga yadda za a aiwatar da shi. Babban matsalar jihar nan ba zababbun shugabannin kananan hukumomi, su kuma masu rikon kananan hukumomin ba su karfin taba kudaden, amma gwamnan jiha ya bada tabbacin za a yi zaben kananan hukumomi nan ba da jimawa ba.

Da zaran an yi zabe a lokacin ne jama’a zasu taka rawar ganin su, za mu tabbatar mun hada kai da kungiyar shugabannin kananan hukumomi ta hanyar ba su shawarwari ta yadda ba su je suna aikin baban giwa ba. Babban abinda jama’a ke bukata, bai wuce samar da tsaftataccen ruwan sha ba, samar da hanyoyi a garuruwa da karkara, tsarin kiwon lafiya mai inganci da kayan aiki, da kuma inganta tsarin ilimi a yankunan kananan hukumomi da kayan aiki. Ina da tabbacin idan aka inganta wadannan bangarora a kananan hukumomi za a samu cigaba sosai, za mu sanya idanu kuma za mu hada kai da su.

Maganar karancin albashi dai, gwamnatin Muhammadu Buhari ta sanya hannu aka naira dubu talatin a matsayin mafi karancin albashi, amma akwai abubuwa da dama da ba a walwale su ba, misali an ce lallai dole sai mafi karancin albashi ya kai naira dubu talatin, to wadanda albashin su ya wuce dubu talatin din fa, ba a yi magana akan wannan ba, saboda haka mu cigaba da tattaunawa akan wannan lamarin, abinda shugaban kasa ya sanyawa hannu aikin takarda ne kawai, hakikanin yadda za a gudanar da tsarin muna cigaba da tattaunawa akai, domin kowa ya anfana da wannan tsarin na mafi karancin albashin. Yanzu muna jiran umurni ne daga uwar kungiya ta kasa dan mu san abin yi, dan gane da abinda ke faruwa in tattaunawa bai yiwu ba zamu dauki mataki na gaba.

An bayyana cewar kungiyar ma’aikatan kananan hukumomi tana zama dan tantance tsarin mafi karancin albashin ma’aikatan kananan hukumomi na naira dubu talatin ga mafi karancin albashi. Shugaban kungiyar ma’aikatan kananan hukumomi ( NULGE) reshen jihar Neja, Kwamared Idris Abdulkareem Lapene ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai kan mafi karancin albashin ma’aikata a minna fadar gwamnatin Neja. Lapene yace akwai ma’aikatan da albashin su yafi karfin wannan tsarin dole sai an zauna an tantance kafin ya fara aiki, wanda yanzu haka muna kan tuntubar hukumomin da abin ya shafa dan yin nazari daidai da yadda dokokin kasa ya tanadar kan albashin ma’aikata.

Da ya juya kan kudaden kananan hukumomi da ake zargin gwamnatocin jahohi na dan newa kuwa, yace sama da shekaru hudu muke ta yekuwar gwamnatocin jahohi su sakar wa kananan hukumomi mara ta yadda zasu samu damar gudanar da ayyuka a bangarorin kananan hukumomin su, domin mutanen da ke matakin kasa da yankunan karkaru ba sa samun damar samun abubuwan more rayuwa da ya ta’allaka ga shugabannin kananan hukumomi su samar masu.

Ya ce a matakin kungiyar ma’aikata muna sanya idanu akan yadda ake gudanar da mulki, a satin da ya gabata mun hadu da NFIU mun kuma sanar masu cewar abinda yake faruwa ba shi ne tsarin da aka yi na baiwa kananan  hukumomi kudaden su ba, domin gwamnati na baiwa kananan hukumomi kudaden su da hannun dama suna karbewa da hannun hagu, kuma ita NFIU sun yi alkawalin bada sabon tsari kuma zai tafi kai tsaye ga bankuna, yadda su kuma zasu bi tsarin tafiyar da kananan hukumomi. Aikin zai tafi ne kai tsaye zuwa kungiyar mu, domin mu zamu sanya ido mu ga yadda kananan hukumomin za su karbi kudaden da yadda zasu kashe su, wanda da zaran an dawo hutun sallah za mu baiwa dukkanin kananan hukumomi wannan sabon tsari kuma za mu tabbatar mun sanya idanu mu ga yadda za a aiwatar da shi.

Babban matsalar jihar nan ba zababbun shugabannin kananan hukumomi, su kuma masu rikon kananan hukumomin ba su karfin taba kudaden, amma gwamnan jiha ya bada tabbacin za a yi zaben kananan hukumomi nan ba da jimawa ba. Da zaran an yi zabe a lokacin ne jama’a zasu taka rawar ganin su, za mu tabbatar mun hada kai da kungiyar shugabannin kananan hukumomi ta hanyar ba su shawarwari ta yadda ba su je suna aikin baban giwa ba. Babban abinda jama’a ke bukata, bai wuce samar da tsaftataccen ruwan sha ba, samar da hanyoyi a garuruwa da karkara, tsarin kiwon lafiya mai inganci da kayan aiki, da kuma inganta tsarin ilimi a yankunan kananan hukumomi da kayan aiki. Ina da tabbacin idan aka inganta wadannan bangarora a kananan hukumomi za a samu cigaba sosai, za mu sanya idanu kuma za mu hada kai da su.

Maganar karancin albashi dai, gwamnatin Muhammadu Buhari ta sanya hannu aka naira dubu talatin a matsayin mafi karancin albashi, amma akwai abubuwa da dama da ba a walwale su ba, misali an ce lallai dole sai mafi karancin albashi ya kai naira dubu talatin, to wadanda albashin su ya wuce dubu talatin din fa, ba a yi magana akan wannan ba, saboda haka mu cigaba da tattaunawa akan wannan  lamarin, abinda shugaban kasa ya sanyawa hannu aikin takarda ne kawai, hakikanin yadda za a gudanar da tsarin muna cigaba da tattaunawa akai, domin kowa ya anfana da wannan tsarin na mafi karancin albashin. Yanzu muna jiran umurni ne daga uwar kungiya ta kasa dan mu san abin yi, dan gane da abinda ke faruwa in tattaunawa bai yiwu ba zamu dauki mataki na gaba
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: