Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Ranar Firgici A Legas: Matar Aure, Direban Bas, Ma’aikacin Banki Duk Sun Kashe Kansu

Published

on

jiya ne abubuwan firgici da tayar da hankali su ka yi ta faruwa a garin Legas, inda da farko a ka sami wata matar aure mai suna Omolara Nathaniel ta rataye kanta a jikin fankar silin ta mutu, hakan ya afku ne a unguwar Egbeda ta cikin garin Lagos din da misalin karfe 3 na yammacin ranar a wani gida mai lamba 5 da ke kan titin Adewole.

Duk da shi ke har kawo hada wannan rahoton babu wani cikakken bayani a kan dalilin kashe kanta da matar ta yi, wani da lamarin ya auku a kan idonsa ya ce, matar wacce ta ke da haihuwar da guda daya, ta na fama ne da ciwon damuwa na tsawon shekaru har zuwa lokacin da ta yanke shawarar kashe kan nata a bisa dalilin da ba ta bayyana ba. an ce matar tana ta faman zuwa karban magani a bisa cutar damuwar da ke damun nata, wanda har hakan ya kaita ga komawa gidan iyayenta na dan wani lokaci domin jinya a kwanan nan.

A cewar ganau, wanda ya roki da a sakaya sunansa, Omolara da mijin nata, Bola suna zaune a gida guda kafin ta koma wajen iyayen nata a kwanan nan, wanda daga bisani ta komo dakin na su mai ciki guda domin ci gaba da shan magani.

Sai dai a lokacin da mijin nata ya ruga domin siyo mata wasu magunguna, dawowarsa ne ya iske ta ta na reto shake a jikin fankar Ceilling din dakin na su, inda duk wani kokari da mijin ya yi na ganin ya ceci ranta abin ya ci tura.

Jami’an karamar hukumar da su ka ziyarci wajen ne suka bayar da izinin a yi mata jana’iza.

Haka nan, wani direban motar haya ta bas mai suna Kabiru Bello an yi zargin ya kashe kansa a wani garejin gyaran motoci da ke can Lagas, a ranar Asabar. Bello, wanda yake da zama a gida mai lamba 77, a kan titin Owode Ibeshe, da ke Unguwar Ikorodu, an yi zargin ya kwankwadi maganin kashe kwari ne da ake kyautata zaton na Sniper ne a cikin garejin da ke tashar mota ta, Ladylack bus stop, da ke Somolu, da misalin karfe 1 na rana, da nufin ya kashe kansa.

An ce, Bello ya na zaune ne a cikin motar bas din na shi mai lamba, AKD724DM, a lokacin da ya kwankwadi maganin kwarin. An ce mutanan da suke a cikin garejin sun yi kokarin garzayawa da shi zuwa Asibitin Adesola Clinic da ke Somolu, inda isar su aka sanar da su ai har ya cika.

A cewar Kakakin rundunar ‘yan sanda, DSP Bala Elkana, masu binciken zargin kashe kai daga rundunar sun ziyarci wajen da abin ya auku, inda suka gano kwalbar maganin kwarin ta Sniper wacce babu komai da ya saura a cikinta, amma sun tabbatar da cewa, a baya akwai maganin kwarin na Sniper a cikinta, ya kara da cewa, tuni sun kai gawar na shi wajen bincike a dakin ajiyar gawarwaki.

A kuma wani abin tashin hankalin duk mai kama da wadannan, wani ma’aikacin Banki mai shekaru 46, shi ma ya kashe kansa ta hanyar kwankwadar guba a cikin dakinsa da ke Unguwar Bictoria Island, Lagos. Mutumin mai suna, Onyechere Ibeakanma, wanda yake da aure har da haihuwar diya mace guda, an yi zargin ya kashe kansa ne a ranar Juma’a, 9 ga watan Agusta, bayan ya bar ‘yar wata takarda mai dauke da sako ga matarsa mai suna Cecilia, wacce ta fita zuwa kasuwa siyo wasu abubuwa.

A cikin takardar sakon da ya bari wa matar na shi, mutumin wanda manajan hulda da mutane ne a daya daga cikin shahararrun Bankunan zamani, cewa ya yi, ìAbu mafi dacewa, shi ne abin da na saba kiranki da shi. To a karshe dai, wannan shi ne karshen rayuwata a doron duniya. Mugun abin da nake ta kokuwa da shi dai ya rinjaye ni wajen kashe wutar da ke ci na. Kina auren mutumin da bai dace ne ba. Ke mata ce mai mutunci, kin kuma cancanci duk wani abu mai kyau. Akwai bukatar ki kasance a cikin farin ciki. Akwai bukatar ki sami hutu.

Don Allah ki kula da rayuwar gimbiyarmu, Chinenyenwa.  Ki shaida mata ina matukar sonta sosai. Ki kasance cikin lumana da kowa, duk da cewa hakan ba abu ne mai sauki ba. ki shaidawa dangi na kar su kullaci wani abu mara kyau a tare da ke. Ke albarka ce a garemu. Wannan shi ne wasiyyar mutumin da ke kan hanyar mutuwa. Kar ki yi mani kuka, amma ki yi mani addu’a ne. ina matukar sonki tare da diyarmu Chinenye, matukar gaske. Sai watarana abar kaunata.î

A cewar wata majiya ta iyalansa, mamacin, Onyechere, ya bar milyoyin naira a cikin daya daga cikin asusun ajiyarsa na Banki, kan haka ne shawararsa na kashe kansa ta girgiza mutane masu yawa. Sai dai majiyar ta yi nuni da cewa, sau tari ma’aikacin bankin yakan nuna wasu bakin halaye da dabi’u, wadanda ba wani cikin dangin na shi da ke daukan su da mahimmanci har sai lokacin da ya mutu.

Wani kuma labarin shigen wannan, shi ne na wani dalibin Jami’a dan aji uku shi ma da ya kashe kansa, a bisa abin da ya kira da, ìRashin samun kulawa daga wajen iyayensa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!