Connect with us

RIGAR 'YANCI

Sarkin Bichi Ya Nada Mawaki Aminu Ala Sarautar Dan Amanar Bichi

Published

on

A jiya Litinin ne, Mai Martaba Sarkin Bichi, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya yi  bikin nada fitaccen mawaƙin nan Aminuddeen Ladan Abubakar (Ala), a matsayin Dan Amanar Bichi, wato Sarautar Dan Amanar Bichi.

Wannan shi ne nadin Sarauta ta farko da Sarkin na Bichi ya yi tun bayan lokacin da Gwamnatin Jihar Kano, ta amince da nada shi a matsayin Sarkin na Bichi a ‘yan watannin da suka gabata.

Har ila yau, kamar dai yadda Aminin mawakin Aminu Ala, Alhaji Auwalu Garba Dan Borno, ya bayyana mana jim kadan bayan aiwatar da wannan nadin Sarauta, ko kadan wannan Sarauta ba ta da wata alaka ta kusa ko ta nesa da waka, ma’ana, ba waka ce ta sa Mai Martaba Sarkin Bichi, ya nada shi wannan Sarauta ba, sannan ita ma wannan Sarauta ce mai cin

gashin kanta.

Dan Borno, ya taya Aminin nasa Ala, murna bisa samun wannan Sarauta da ya yi, tare da godiya ga Allah da kuma Mai Martaba Sarkin na Bichi, sakamakon karrama wannan Amini nasa a matsayin mutum na farko day a fara nada wa ko baiwa Sarauta a wannan Masaurata ta Bichi. Ya kuma yi addu’ar Allah Ya taya shi riko Ya kuma ja da ran Mai Martaba Sarki.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: