Connect with us

Uncategorized

Shugaban Kungiyar Manoman Shinkafa Ya Taya Yayan Kungiyar Murnar Sallah

Published

on

 

Shugaban kungiyar manoman Shinkafa ta kasa reshen jihar Kaduna  Alhaji Muhammad Umar Dangaladiman Numbu  ya taya manoman Shinkafa dake daukacin fadin kasar nan murnar yin salla babba. Alhaji Muhammad Umar Dangaladiman Numbu   ya bayyana hakan ne a cikin sanarwar da mai yada labaran kungiyar  Alhaji  Abubakar Zakarai ya baiwa jaridar Leadership A Yau a Kaduna. Shugaban ya kuma yi kira ga daukacin Musulmai dake cikin fadin duniya dasu koyi da mahammancin ranar ta sallah, musamman a kan gwajin da Allah ya yiwa Annabi Ibrahim AS.

Ya yi kira ga daukacin maoman Shinkafa dake cikin fadin kasar nan, musamann  na jihar Kaduna, dasu kara zage damtse wajen wajen bayar da tasu gudunmawar wajen ciyar da kasar nan gaba. Dangaladiman Numbu  ya kuma jinjiwa Shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan kokarin sad a yake yi wajen ganin an wata kasar nan  da abinci da kuma wanda za’a fitar dashi zuwa kasuwannin dake kasashen duniya. Ya kara da cewa, kungiyar ta samar da Shinkafa sama da buhu dubu 11 daga hannun yayanta a kakar noman bara. Alhaji Muhammad Umar Numbu, ya ce Shinkafar da yayan kungiyar suka noma a daminar bara ne a karkashin shirin noman Shinkafa da Gwamnatin Tarayya ta samar domin tallafa wa manoman.

A cewarsa, nan da shekara mai zuwa kungiyarsa, za ta wadata Jihar Kaduna da abinci da kuma kasa baki daya sakamankon jajircewar yayan kungiyar suka yi wajen noman ta. Ya koka, a kan yadda wasu daga cikin yayan kungiyar suka gaza  cika alkawarin da suka dauka bayan sun ci  bashin tallafin noman Shinkafa a Jihar. Alhaji Muhammad Umar Numbu, ya ce kashi goma cikin dari ne kawai cal na wadanda suka amfana da bashin noman shinkafar suka iya biyan bashin a jihar. Ya kara da cewa, da yawa daga cikin manoma sun dauki shirin a matsayin tallafi ne na Shugaba Buhari, da aka ba su kyauta ba bashi ba.

A  cewarsa, hakan ne ya sanya  suke ta wayar da kan ’ya’yan kungiyar nasu don su fahimci yadda shirin yake, domin duk wanda aka ba shi kayan aikin noman Shinkafa don ya biya ne a cikin shekara daya. Shugaban ya kara da cewa, ya zuwa yanzu shirin ya samu tarnaki a jihar saka

makon ambaliyar ruwa, da kuma matsalar tsaro da aka yi fama da ita a bara. Shugaban ya ce, hakan ya hana manoma da yawa zuwa gona a daminar bara, kuma hakan ya sa da yawa daga cikin manoman suka kasa biyan bashin da suka ci don noman Shinkafa a jihar. A cewarsa, wannan ne

ya sa suka zauna da Babban Bankin CBN  da Bankin Manoma, inda suka cimma matsaya ta sakarwar na manoman mara da sukaci bashin suka kuma gaza biya. Alhaji Muhammad Umar Numbu, ya ce a dalilin haka kungiyar ta zauna da babban lauyansu; inda ya ba su shawarwari na su ba manoman

takardun tuntuba da tsaida lokaci don maido da bashin da suka ci. A karshe, Alhaji Muhammad Umar Numbu ya shawarci yayan kungiyar su yi amfani da wannan dama wajen bunkasa noman Shinkafa da ciyar da jihar da kuma kasa gaba a kakar daminar ta 2019.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!