Connect with us

DAGA BIRNIN SIN

Sin Ba Za Ta Lamunci Shisshigin Da Kasashen Waje Suke Yi A Hong Kong Ba

Published

on

Tashe-tashen hankali na ci gaba da taazzara a yankin Hong Kong na kasar Sin a yan kwanakin nan, inda wasu kasashen yammacin duniya ciki har da Amurka suka kara hura wutar rikici da tunzura masu tsattsauran raayi, da zummar tsoma baki cikin harkokin cikin gidan yankin na Hong Kong.
Babu shakka, duk wata kasa mai cikakken yanci ba za ta yi biris da irin wannan mummunar aika-aikar da wasu yan siyasar kasashen yammacin duniya suka yi ba. Kasar Sin ita ma ba za ta lamunci duk wani shisshigin da wasu kasashe suka yi don hura wutar rikici gami da lalata yankin Hong Kong ba.

Tun da wasu masu tsattsauran raayi a Hong Kong suka tada wutar rikici bisa hujjar yin gyare-gyare ga dokar tasa keyar wadanda suka yi laifi zuwa babban yankin kasar Sin a watan Yunin bana, ya zuwa yanzu, wasu yan siyasar kasashen Amurka da Birtaniya sun yi yunkurin shiga sharo ba shanu cikin harkokin yankin na Hong Kong. Tsohon ministan harkokin wajen Birtaniya Jeremy Hunt ya bukaci a gudanar da bincike kan tashe-tashen hankalin da suka faru a ranar 12 ga watan Yuni a Hong Kong, kana, mataimakin shugaban kasar Amurka gami da sakataren harkokin wajen kasar sun gana da wasu mutanen Hong Kong dake adawa da gwamnatin tsakiya ta kasar Sin gami da tada zaune-tsaye a wajen, har ma akwai wasu yan siyasar yammacin duniya wadanda ke fakewa da dalilan da suka shafi kare hakkokin da Adam da shimfida tsarin demokuradiyya don fito da maaunai biyu. Wato, sun yi yunkurin jirkita gaskiya da sanya jamaa su kasa fahimta tsakanin aikin nuna karfin tuwo da yin zanga-zangar lumana, da hura wutar rikici a Hong Kong, tare kuma da shafawa gwamnatin yankin Hong Kong gami da yan sandan wurin kashin kaji, wadanda suka gudanar da ayyukansu daidai bisa doka da oda, da zargin gwamnatin tsakiya ta kasar Sin da cewa tana rage yancin kai da hakkokin mutanen Hong Kong, duk wadannan alamuran da ba safai a kan gansu ba a duniya.
A kwanakin nan, wasu kasashen duniya na kara tsoma baki cikin harkokin cikin gidan yankin Hong Kong. Har ma ministan harkokin wajen kasar Birtaniya Dominic Raab ya yi wani abu tamkar tsohon mai mulkin mallaka, inda har ya bugawa kantomar yankin Hong Kong waya kai tsaye don matsa mata lamba. Gaskiya bai cancanta ba sam! Haka kuma an wallafa wasu hotuna a shafin intanet dake nuna cewa, wata jamia daga ofishin jakadancin Amurka dake Hong Kong ta tuntubi wasu jagororin wadanda suke yunkurin balle Hong Kong daga kasar Sin, inda kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurkar ya yabawa hakan. Irin wannan aika-aikar da Amurka ta yi na tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasar Sin, ya keta dokokin kasa da kasa gami da ka’idojin da suka shafi dangantakar kasashen duniya, abun rashin mutunci ne kawai.

Tashe-tashen hankulan da suka ki ci suka ki cinyewa gami da shisshigin da wasu kasashen waje suka yi sun sa Hong Kong na fuskantar babban hadari. Alal milsali, yawan ribar da aka samu daga sana’ar samar da abinci a Hong Kong ta yi kasa sosai a cikin shekaru 10 da suka wuce, haka kuma sana’ar yawon bude ido ta tabarbare kwarai da gaske. Idan wutar rikici ta ci gaba da ruruwa har zuwa fannonin hada-hadar kudi da cinikayya da jigilar kayayyaki, tattalin arzikin Hong Kong zai fuskanci babbar asara wadda ba za’a iya kimantawa ba.
A halin yanzu yankin Hong Kong na kasar Sin na cikin wani muhimmin lokaci, kuma dakatar da rikici da dawo da zaman lafiya shi ne abun da ya kamata a ba wa fifiko. Miliyoyin mazauna Hong Kong ba za su amince da duk wani shisshigin da kasashen yammacin duniya suka yi a wajen ba.
Gwamnatin kasar Sin na son shaidawa duk duniya cewa, kada wasu kasashe su raina babbar niyyar da gwamnati gami da jama’ar kasar ke da ita wajen kare ikon mallakar kasar da zaman lafiya da kwanciyar hankali gami da cikakken yankinta. Kasar Sin na da duk wata dabara da babban karfi wajen tinkarar duk wani abun da zai wakana a yankin na Hong Kong, kana kuma ya kamata a ce “Ku dakata haka nan” ga kasashen wajen da suka hura wutar rikicin a wurin.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: