Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

‘Yan Sanda A Kasar Sin Sun Kashe Wani Dan Nijeriya

Published

on

Wani dan Nijeriya mazaunin garin Guangzou, ta yankin Guandong, a kasar Sin mai suna Mista Joseph Nwachueze, ya gamu da ajalinsa a sakamakon raunukan da da ya samu a hannun ‘yan sandan kasar ta Sin.

Lamarin ya faru ne a jiya, a lokacin da mamacin wanda ya shafe tsawon shekaru 15 yana zama a kasar ta Sin, ‘yan sandan suka biyo shi.

Matar mamacin, wacce ta fito daga karamar hukumar Idemili, ta Jihar Anambra, an ce ta yi ta suma a lokacin da ta samu labarin mutuwar mijin nata.

Kamar yanda wani shafin yanar gizo mai suna, Akelicious News, ya nuna, mamacin wanda aka ce Limamin Kirista ne, an ce yana da ‘yaíya uku.

An ce ‘yan sandan sun yi amfani ne da wata naíura mai aiki da lantarki, da ake kira da,  electronic torch, wajen tsayar da mutumin, wanda ya kere masu da gudu a lokacin da suke biye da shi, inda a nan take mutumin ya hantsala ya fadi kasa kuma ko shurawa bai yi ba ya ce ga garinku nan.

An ce ‘yan sandan sun yi ta kokarin ganin ko za su iya farfado da shi, amma ina! Tuni rai ya rigaya ya yi halinsa.

A sakamakon hakan ya sanya dandazon ‘yan Nijeriya da ke zaune a garuruwan, Guangyuandilu, Tongtong Plaza, nan take suka yi wo tururuwa bisa kan tituna suna nuna rashin amincewar su.

Sai dai jagoran ‘yan Nijeriya din da ke yankin na Guandong, Mista Festus Mbisiogu, ya yi kira ga ‘yan Nijeriyan da su kwantar da hankulansu, yana mai cewa ka da su dauki doka a hannunsu.

Ya kuma nemi hukumomin kasar ta Sin da su gudanar da bincike a kan yanda lamarin ya faru.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!