Connect with us

BIDIYO

Adam A Zango Ya Shelanta Ficewa Daga Kannywood

Published

on

Shahararrane jarumin finafinan Hausa Adamu Abdullahi, wanda aka fisa ni Adam A Zango, ya ayyana ficewa daga masana’antar Kannywood, inda ya ce daga shi ba dan Kannywood ba ne, illa mai jarumi mai shirya finafinai a qashin kansa.

Kamar yadda ya wallafawa a shafinsa na Instagram, Adam Zango ya ce, babu wata alaqa tsakaninsa da wannan suna na Kannywood. Domin shi yanzu xan wasan Hausa ne mai zama kansa.

A Zango ya rubuta a shafinsa kamar haka: “Daga yau 15 ga watan Agusta (jiya kenan), ni Adam A Zango na fita daga Qungiyar shirya finafinai ta Kannywood. Daga yau duk abinda na aikata mai kyau ko marar kyau ka da a danganta shi da Kannywood. Da gaya yau duk arziki ko rashinsa a Kannywood ba na buqata. Wannan hakkina ne, ka da al’umma su yi min mummunar fahimta. Babu dokar da qungiyoyinta a kaina. Dalili, shugabanci kama-karya da ake yi. Mai qarfi, mai daukaka, mai arziki ba a iya hukunta shi saboda kwaxayi da son zuciya. Na zama independent filmmaker (dan fim mai zaman kansa).
Za mu kawo muku cikakken rahoton nan gaba kadan……
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!