Connect with us

Da dimi-diminsa

Da Dimi-diminsa: El-Zakzaky Zai Dawo Nijeriya Daga Indiya

Published

on

A wani sakon bidiyo mai tsawon minti daya, Shugaban harkar Musulunci a Nijeriya, wadanda aka fi sani da ‘yan uwa Musulmi, Shaikh Ibraheem El-Zakzaky, ya bayyana cewa zasu dawo gida Nijeriya daga birnin Delhi na kasar Indiya.

Malamin wanda ya fita ranar Litinin din da ta gabata daga Nijeriya zuwa kasar Indiya don neman magani, ya bayyana cewa an samu rashin aminci a asibitin da suka je neman magani a kasar ta Indiya. Inda hukumomin kasar ta Indiya suka bashi zabin ko dai ya amince da asibitin ko ua fice daga kasar.

Bayan tattaunawa sai hukumomin kasar suka sanar da tawagar Malamin wacce ta hada sa mai dakinsa Malama Zeenah, wacce ita ma take fama da jiki, cewar hukumomin kasar ta Indiya sun yanke shawarar mayar da tawagar El-Zakzaky din Nijeriya, kuma zasu yi hakan ne cikin daren yau.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: