Connect with us

RIGAR 'YANCI

Ganduje Ya Fi Gwamnonin Kano Yiwa Matasa Kabakin Arziki – Gwarmai

Published

on

An bayyana cewa, ba a taba yi wa Matasa kabakin alhairi wanda Gwamna Ganduje, ya yi musu a wannan babbar Sallar da ta gabata a Jihar Kano ba. Jawabin haka, ya fito daga bakin Mataimakawa Gwamna Ganduje, na musamman kan harkokin siyasa, Alhaji Murtala  Gwarmai, a lokacin da yake gabatar da sakon Gwamna ga daruruwan Matasa a JIhar Kano, inda Gwamna ya bayar da kyautar raguna da shanu domin jika hantar Matasan.

Murtala Gwarmai, ya ci gaba da cewa, ko shakka babu Gwamna Ganduje na yin alfahari da gudunmawar da Matasa ke baiwa wannan Gwamnati, kuma kullum Matasan na cikin zuciyarsa, wannan tasa duk wani sha’ani da a ke gabatar wa da Matasa a sahun gaba. Misali, idan a ka dubi yadda Gwamnatin Ganduje, ke fitar da kyawawan manufofin yadda za a tallafa wa rayuwar Matasan ta hanyar samar da guraban koyon sana’o’i da kuma daukar nauyin karatunsu.

Haka zalika, Gwarmai ya bayyana farin cikinsa a madadin sauran Matasan Jihar Kano, bisa

yadda Gwamna Ganduje, ya tabbatar da aniyarsa ta bayar da ilmi kyauta wanda kuma ya zama wajibi ga kowane dan Jihar Kano, ya samu ilmin. Sannan ya kara jinjina wa Gwamnan da Gwamnatinsa ta Kano, bisa kammala aikin Cibiyar koyar da sana’o’i da ke kan titin zuwa Zariya wadda ita ce ta farko a fadin Nijieriya baki daya. Wannan Cibiya Gwamnatin Kano ta kashe Bilyoyin Naira, domin inganta rayuwar Matasa.

Har ila yau, sakamakon wannan kyakkyawan tagomashi na Gwamna Ganduje, yasa Murtala Gwarmai, ke tabbatar wa da Gwamna cewa, da yardar Allah, Matasa a Jihar Kano, za su ci gaba da baiwa wannan Gwamnati dukkanin goyon bayan da take bukata, sanann kuma ya yi wa Gwamna alkawarin cewa, Matasa ba za su ba shi kunya ba.

A karshe, Alhaji Murtala Gwarmai, ya gabatar da sakon godiyar Matasan Jihar Kano, bisa kabakin alhairin da aka yi masu ta hanyar ba su raguna da shanu, tare da samar musu da abin da za su sarrafa, wannan hidima ta Sallar. Ya ce, “babu shaka, iyalai, iyaye da sauran Abokan arziki, sun yi farin ciki kwarai da gaske da wannan kyautayi na Gwamna Ganduje. Shi yasa suka yi masa fatan samun cikakkiyar nasarar da ya ke bukata a wannan zango nasa na biyu“,  in ji shi.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: