Connect with us

LABARAI

Shugaban Amintattun PDP Ya Goyi Bayan Ruga

Published

on

  • Ba Komai Ake Sa Siyasa Ba – Walid Jibril

Shugaban kwamitin amintattu (BoT) na babbar jam’iyyar adawa a Najeriya, wato PDP, Sanata Walid Jibrin, ya bukaci al’umman Nijeriya da su rungumi shirin gwamnatin tarayya na samar da wuraren kiwo na dindindin, wato Ruga, a sassan kasar, domin bunkasa cigaba mai ma’ana, domin ba komai a ke sanya siyasa a ciki ba.

Sanata Jibrin, wanda ya shaida hakan ga ’yan jarida a jiya a jiharsa ta Nasarawa, ya na mai fadin cewar tsarin samar wa Fulani wurin kiwo a wuri guda zai tabbatar da kyautata zaman lafiya da karin inganta tsaron kasa.

A fadinshi kuma, shirin zai kuma kara bunkasa tsaron abinci, tsaro da kuma kyautata kiwon lafiya hadi ga wuraren da suka samu cin gajiyar yin Ruga a yankunansu.

Jibrin, wanda kuma shi ne Sarkin Fulanin Nasarawa, ya jinjina wa gwamnatin tarayya a bisa gabatar da yunkurinta na samar da Ruga a kasar bisa lura da alfanunsa ga Nijeriya.

A cewar shi, “ni ba dan jam’iyyar APC ba ne, ni jigo ne a jam’iyyar PDP, amma dai idan a na maganar cigaba da tsaro, mu kan ajiye kowani abu da ya shafi siyasa, kalibalanci ko addinanci. Kowaye ke mulki a Nijeriya in ya kawo wani tsari ko shiri da zai yi awun gaba da matsalar tsaro, kashe-kashe, zai kuma tabbatar da jin dadi da walwalan ‘yan kasa, zan mara wa shirin baya. Ni irin salon siyasata ba wai a-yi-ne-ko-a-mutu ba, ina tafiyar da harkokin siyasa ne ba da kiyayya ba.

“Wannan dalilin ni da Fulani muke jinjina wa gwamnatin tarayya na yunkurin samar da Ruga a fadin kasar nan.

“Ni da kabilata (Fulani) mun rungumi shirin samar da RUGA. Wannan shirin ya hada da samar wa Fulani makiyaya asibiti, makarantu, samar da wuta da ruwa, da sauran ababen daban-daban, wadanda kai tsaye za su kyautata rayuwar makiyaya.

“A karkashin wannan shirin, za a rage yawaitar fadace-fadace tsakanin manoma da makiyaya gami da bunkasa abinci da tsaro a fadin Nijeriya,” A cewar shi.

Sanata Walid sai yayi kira ga al’ummar Igbo da Yaruba da sauran kabilu da su rungumi shirin samar da Ruga domin kare martaba da muradin kasar nan.

Yana mai cewa; “sama da jihohi 12 a arewacin Nijeriya ciki har da jihar Nasarawa sun rungumi shirin nan gami da fara shirye-shiryen samar da shi. Don haka muna kiran ‘yan Kudu, Igbo da Yoruba da sauransu, su rumgumi wannan shirin hanu biyu-biyu, duk da yake shi wannan shirin ba dole bane. Ruga zai killace Fulani a wuri guda, samar da zaman lafiya da tabbatar da walwala, wasu jhohin da suke arewa maso gabas sun yi alkawarin bayar da muhalli domin aiwatar da wannan shirin na samar da Ruga,” A fadin Sanata.

Sanata Jibrin, ya roki dukkanin makiyaya da suke fadin Nijeriya da sauran jama’a da su bayar da tasu gudunmawar wajen yakar fashi da makami, garkuwa da mutane da sauran ababen da suke barazana wa zaman lafiyar kasa domin shawo kansu.

Jigo a PDP ya kuma nemi ‘yan Nijeriya da su zauna da junansu lafiya gami da mutunta kabilu, addinai da kuma banbanci na siyasa domin tabbatar da gina kasa mai cike da albarkatu.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: