Connect with us

Uncategorized

Tattalin Arziki: Gwamnatin Kano Za Ta Hada Gwiwa Da Kasar Guinea

Published

on

A cigaba da kokarin tabbatar da samun ingantaccen tattalin arzikin da ake bukata a yankunan Kasashen Afrika, Gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya gudanar da taron tattaunawa a kan harkokin cinikayya tsakaninsa da Shugaban Kasar Guinea, Farfesa Alpha Conde, tare da sauran ‘Yan Kasuwar Jihar Kano. An dai gudanar da wannan katafaren taro ne a Fadar Gwamnatin Jihar Kano, a ranar Talatar da ta gabata.

Haka zalika, Gwamnan Jihar Kanon, ya bukaci samar da wani bigire wanda zai taimaka wa ‘Yan Kasuwar Jihar Kano, don samun damar zuba hannayen jari a Kasar ta Guinea. Kazalika, Gwamnan, ya bukaci  Kasar ta Guinea ta shigo Jihar Kanon, domin zuba nata hannun jarin. An dai tsara wannan ganawa ne, domin bayar da dama ga al’ummar Jihar Kano da kuma ‘Yan Kasuwar Kasar ta Guinea, wanda ya hada da Ministoci domin gudanar da taron gaba-da-gaba don tattauna hanyoyin da za a bi domin sake habaka tattalin arzikin Jihar Kano da kuma nasu.

Har ila yau, Shugaban Kasar ta Guinea, ya tabbatar wa da daukacin al’ummar Jihar Kano cewa, a kodayaushe a shirye suke wajen karbar ’Yan Kasuwar Kano, tare da yi musu lale marhaban domin samar musu da guraban zuba hannayen jari a cikin fadin Kasar tasa. Daga nan kuma, ya sake jadadda cewa, “kasancewarmu a matsayin ‘yan’uwan juna daga Afrika, ina tabbatar maku da cewa, ba kuda wata matsala wajen zuba hannayenku na jari a dukkanin bangarorin da kuke bukata a Kasarmu ta Guinea”, in jishi.

Daga  nan, Shugaban Kasar Guinea, ya kara da cewa, a Kasarsa ta Guinea, ‘Yan Kasuwar Kano, ba za su fuskanci wani banbanci na mu’amala ko wani abu mai kama da wannan ba, musamman a bangaren harkokin kasuwanci. “Babu batun kabilanci ta fuskar matakan samun damammaki, kowace iri ce kuwa, abin da muka amince da shi, shi ne nagarta.”

Haka nan, ya sake karfafa wa ‘Yan Kasuwar Kano guiwar da cewa, Kasarsa na da sauki matuka a fannin tsarin kasuwanci. Haka zalika, ya kara tabbatar da cewa, tun zuwansa karagar mulkin Kasar a shekara 2010, yake yin bakin kokarinsa, wajen tabbatar da gaskiya da kara inganta harkokin tattalin arzikin kasa.

Da ya ke gabatar da nasa jawabin, Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje cewa ya yi, “na yi matukar gamsuwa da jawabin Shugaban kasa, sannan ya jadadda aniyarsa ta ci-gaba da tattaunawa da wakilan Shugaban Kasar da sauran ‘Yan Kasuwa na Jihar Kano, dangane da wadannan damammaki da ake da su a harkokin ciniki da Kasar ta Guinea da ma sauran batutuwa”, in Gwamnan.

Ya cigaba da cewa, matsayin da Jihar Kano ke da shi a fannin kasuwanci ta fuskar ci-gaban tattalin arziki a ciki da wajen kasar nan, shi ake hange a Nijeriya, ‘Yan Kasuwar Kano a yau na da wani matsayi a Nijeriya da ma duniya baki daya.”

Ganduje ya kara da cewa, “a wasu shekaru da suka gabata, akwai kyakkyawan ci-gaba da kuma tabbacin da ake da shi a kan al’ummar Nijeriya, na wani matsayin mai kyau a sassan duniya. Wannan abin alfaharinmu ne a Jihar Kano a yau, Bakin Mutumin da ya fi kowa kudi a Afrika, dan asalin Jihar Kano ne, Alhaji Aliko Dangote, GCON.”

Saboda haka, domin tabbatar da cewa, a shirye muke kan batun tattalin arziki a wannan zamani, Gwamna Ganduje ya shaida wa Shugaban Kasar ta Guinea cewa, “harkokin kasuwanci da ciniki, sama da shekaru masu yawa shi ne abin da aka san birnin Kano da shi. Fatake, masu yawon bude ido, ‘Yan Kasuwa, Malamai da sauran manyan mutane a duniya, sun jima suna tururuwar shigowa Jihar Kano, domin amfana  da karamcin Kanawa.

“Babban abin da ke daukar hankalin duniya da kuma abubuwan amfani da Allah (SWT) Ya jibge a Kano, yasa jama’a daga sassan Nijeirya, Afrika, Daular Larabawa da kuma Turawan Yamma ke tururuwar zuwa Kano, domin bude ido  da kuma harkokin tattalin arziki”, a cewarsa.

Gwamna Ganduje, ya sake tabbatar wa da Shugaban Kasar na Guinea cewa, Gwamnatin Kano a kodayaushe a shirye take domin aiki tare da Kasar ta Guinea, don karfafar juna da kuma kara dankon zumunta a tsakaninsu.

Haka zalika, shi ma Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya bayyana nasa farin cikin bisa wannan yunkuri na kara dangantaka tsakanin Jihar Kano da kuma kasar Guinea. Sarkin ya kara da cewa, irin wannan alaka za ta taimaka matuka wajen rage kwararar ‘Yan

gudun hijira zuwa wasu sassa na duniya, musamman Kasashen Turai da kuma sauran Kasashen da su ka cigaba.

“Dole ne kasancewarmu mutane, mu tabbatar da ganin irin wannan hasken ya ci-gaba, sannan wajibi ne al’ummar Kasashen Afrika, su rungumi ‘yan’uwansu ‘Yan Afrika, ba wasu na wani bangare daban ba, ta haka ne za mu iya samar da ingantaccen matakin yakar matsalar fatara”, in ji Mai Martaba Sarki.

Haka nan, shi ma shahararren Attajirin nan, dan asalin Jihar Kano, ya halarci wannan taro ko  tattaunawa, Alhaji Aliko Dangote, wanda Injiniya Mansur Ahmed, ya wakilta, sai kuma Alhaji Tajuddeen Dantata, wanda ya wakilci rukunin Kamfanonin Dantata, Alhaji Nafi’u Isyaka Rabi’u, wanda ya wakilci rukunin Kamfanonin BUA, Shugaban Kamfanin Azman, Alhaji Abdulmanafi

Sarina, Shugaban Kamfani iskar gas, Alhaji Auwalu Ilu da kuma wakilan Kamfanin Gongoni da Kamfanin W.J Bush, duk sun samu damar halartar wannan ganawa. Kamar yadda Babban Sakataren yada Labaran Gwamna, Abba Anwar Ya shaida wa LEADERSHIP A YAU.

 
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: