Connect with us

NISHADI

Fim Din Hauwa Kulu Ya Kara Daga Darajar Kannywood – Maishadda

Published

on

Babban Furodusan finafinan Hausa, Abubakar Bashir Maishada ya bayyana cewar sabon dinsa mai suna Hauwa Kulu, wanda yanzu haka ake ci gaba da nuna shi a Sinima da ke Ado Bayero Mall, ya kara daga darajar Kannywood. A cewarsa, ya yi farin ciki matuka da gaske yadda al’umma masu sha’awar kallon finafinan Hausa suke fitowa kwansu da kwarkwata domin kallon fim din.

Maishadda ya ce, a zahiri kwalliya ta biyan kudin sabulu, domin dama an shirya fim din ne domin mutane su kalla, kuma Alhamdulillah kullum dubunnan mutane ne ke tururuwa zuwa Sinima domin more kallon.

“Hakika babu abinda za mu yi wa Allah sai godiya. Mun shirya fim din Hauwa Kulu don al’umma, kuma al’ummar ta amsa kira. Babu abinda za mu ce sai godiya. Kamfaninmu na Maishadda Global Resources ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen ci gaba da shirya finafinan mai kyau ba.” In ji Maishadda.

Har ila yau ya ce, dama ya yi tsammanin hakan za ta kasance, domin sai da ya shirya sosai kafin kaddamar da fim din Hauwa Kulu.

“Ban yi mamakin nasarar da fim dina ya samu ba. Mun shirya kuma mun yi tsari sosai kafin mu kaddamar da shi. A cikin finafinai kusan 10 da na kai Sinima, babu wanda ya samu karbuwar Hauwa Kulu ya samu. Daga ranar Sallah zuwa yau, dubunnan mutane ne suka yi tururuwa domin kallonsa.”

A ranar Sallah ne dai kamfanin Maishadda Global Resources ya saki sabon fim dinsa mai suna Hauwa Kulu, a Filmhouse Cinema da ke birnin Kano, wanda zuwa yanzu yake samu karbuwa da yabo a wurin makallata finafinan Hausa, musamman yadda ake tururuwa zuwa kallo.

Fim din wanda aka shirya shi a kan matsalar fyade da cin zarafin mata, ya samu tsararren labari daga Fauziyya D Sulaiman, Abubakar Bashir Maishadda ya shirya, yayin da Ali Nuhu ya bada umarni.

Masana, marubuta, masharhanta da ‘yan jarida sun yaba matuka da gaske bisa tsarin da aka bi wajen isar da sako kan wannan babbar matsala da take damun al’ummar Najeriya, ta yadda kullum labaran fyade da cin zarafin mata ke yawo a kafafen sadarwar zamani.

Shugaban Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano, Alhaji Isma’ila Na’Abba Afakallah, ya yabawa kafatanin jaruman da suka fito a cikin fim din Hauwa Kulu, inda ya ce sun taka rawar gani da suka cancanci yabo ta kowace fuska.

Darakta Ishak Sidi Ishak na cikin mutanen da suka yabi fim din Hauwa Kulu, har ma ya ce rabon da ya ga fim din Hausa da ya yi ma’ana irinsa ya kwana biyu. Saboda haka ya jinjina ga wadanda suka shirya da tsara fim din.

Aminu S Bono kuwa, cewa ya yi fim din Hauwa Kulu ya zama kalubale ga dukkanin masu shirya finafinan Hausa, domin su rika duba labaran da suke da alaka da al’umma domin shirya fim ta hanyar fadakarwa da nishadantarwa.

A nasa bangaren, Darakta Hafizu Bello, jinjina ya yi ga furodusa, darakta da kuma jaruman da suka fito a cikin shirin, inda ya ce  lallai Kannywood tana kara girma musamman a wannan yanayi da ake bukatar finafinai masu ma’ana.

Hauwa Kulu labari ne na wata yarinya mai tsananin son karatu, ta gamu da shaidancin wani matashi da ke ta mata mutuncinta. A bisa al’adar kauyen da yarinyar ta so, hakan ya sanya ta rika samun tsangwama da kyara, lamarin da ya kusan jefa rayuwar cikin gagari. Tsayuwar da mahaifanta da saurayinta a bahallatsar shi ne abin da ya bata damar fita daga cikin yanayin.

Babban abun jan hankali a cikin shirin Hauwa Kulu shi ne hukunci da aka yankewa wanda ya aikata laifin duk da cewa yana matsayin da ga alkalin da ake gudanar da shari’ar.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: