Connect with us

RAHOTANNI

Kungiyar Dalibai Musulmi Ta Shirya Wa ‘Yan Sakandaren Bomala Walima

Published

on

Kungiyar dalibai musulmi ta Najeriya MSSN reshen karamar sakandaren Bomala, ta shiryawa daliban ta walimar kammla karatu na karamar sakandare.

Shugaban Makarantar Malam Sa’idu Shehu Mohammed, yace basa fatan dan Yaran sun kammala karamar sakandare shi kenan sun gama karatu ba akwai sauran aiki a gaban su yanzu suka fara su ci gaba har zuwa Jami’a dan wata rana su zama sune malaman.

Malam Sa’idu Shehu, ya kara da cewa amfanin karatu ba kawai a baka Satifiket bane yana koyar da Ilimi da kuma tarbiya na yadda za su kula da rayuwa cikin wayewar kai.

Babban Limamin Juma’a na Bomala, Malam Umar Muhammad Saminu, jan hankalin Daliban ya yi da su zama masu biyayya ga iyaye da Malaman su har ma da wadanda suke  gaba dasu.

Ya kuma ce yana da kyau duk Dalibin da yaje Makaranta Iyayensa su dinga bibiyar karatun da aka koya masa dan tabbatar da kwazon Yara kar a bar su kara zube.

Shugaban Sashin Firamare har ila yau kuma Mai Unguwar Bomala, Malam Ali Jauro, kiran Daliban ya yi da cewa su mayar da hankaki wajen karatu idan suka tafi Babbar Sakandare.

Ustaz Abubakar, nasiha ya yi kan Ilimi da tarbiya inda ya fadakar da Daliban cewa su gane basu da masoya Kamar Malaman su amma yanzu za su ga Kamar takura su ake yi dole suyi karatu.

Wakilin Iyayen Yara Lawan Siraka, kira ya yi musamman ga ‘ya’ya Mata da su zurfafa ilimin su domin idan mace ba ta yi karatu ba yanzu ba mai auren ta da daraja.

Daga nan sai ya yi kira ga iyayen Yara da cewa idan Yaro yaje gida yace Makaranta na neman iyayen Yara dan yi taro su daure suna amsa kira dan tattauna muhimman abubuwa na ci gaba.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: