Connect with us

MU KOYI ADDINI

Mene Ne Hukuncin Yin Alfarma A Asibitoci?

Published

on

Tambaya:

Assalamu alaikum warahmatullahi wa barakatuh, Allah ya karawa malam imani, tambaya zan yi game da ma’aikata musamman na asibiti. Idan abokin aiki ya zo da Mara lafiya sai a yi amfani da sanayya a sallame shi da wuri alhali akwai wadanda suka Dade a layi, sannan kuma suna cewa wai alfarma ce ta tsakanin abokan aiki, shin ya hukuncin yin hakan, kuma shin ba hakkin wadanda suke layi idan har ba a nemi izinin su ba? Allah ya bawa malam damar amsa mana.

Amsa:

Wa’alaikum assalam, Mutukar yanayin ciwonsu iri daya ne, babu bambancin tsanani ko hauhawar ciwon bai halatta a gabatar da wani Mara lafiya akan wani, saboda kusancinsa da likita, ya wajaba a jera su gwargwadon zuwansu.

Hukuma ta dauki ma’aikaci ne don ya yiwa jama’a aiki, ba tare da nuna Bambanci ba a tsakaninsu. Ana biyan Likita ne da kudin al’umar da yake yiwa aiki, don haka zalunci ne ya fifita wani sashe akan wani sashen na jama’a, saboda dukkansu matsayinsu iri daya ne.

Rikon amana yana jawo cigaban rayuwa.

Allah ne mafi sani.

 

Fatawar Rabon Gado (45)

Tambaya:

Assalamu alaikum malam tambaya akan rabon gado. Mutum ne ya rasu Bai da da ko daya Sannan kuma yana da yan’uwa, daya daga ciki mace ce wanda suke uwa daya uba daya. Sai sauran kuma da namji daya da mata uku wanda suke uwa daya. Shin ya rabon gadon xai kasan ce ?.

Amsa:

Wa alaikum assalam, Za’a raba abin da ya bari gida: 5, a bawa ‘yar’uwarsa shakikiya kashi: 3, sai a bawa ‘yan’uwansa da suka hada uwa daya kashi: 2.

Allah ne mafi sani .

 

Hukuncin Fadin “Balaa” A Qarshen Suratu Attin

Tambaya:

Assalam alaikum warahmatallah Malam dafatan kana lafiya amin. Malam akwai addua da akeyi a yayin da aka karanta Suratin Tin a karshen surar wato “Balaa nahanu ala zalika laminash shahideen”. Ya ingancin wannan addua yake? Wassalam Allah ya kara lafiya.

Amsa:

Wa’alaikum assalam, akwai hadisin da Abu-dawud ya rawaito mai lamba ta (887) wanda ya tabbatar da hakan, saidai malaman hadisi sun raunana shi kamar Nawawy a cikin Al-majmu’ú 3/563.

Saidai wasu daga cikin malaman Malikiyya sun só fadin hakan in an karanta karshen Surar WATTIN, hakanan wasu a cikin  Hanabila.

Allah ne mafi sani.

 

Fatawar Rabon Gado(46)

Tanbaya:

Assalamu alaikum. Don Allah a taimaka min da amsa wannan Tambayan. Mu shida a gurin mahaifiyar Mu toh Allah yayi wa daya a chikin Mu rasuwa. Mahaifun Mu Allah yayi masa rasuwa Shima. Toh Wadda ta rasu a chikin Mu. Muna da gadonta ko Dai na mahaifiyar Mu ne kawai ?. Kuma muna da Yan uba ko suma suna da gadonta ?. Dun Allah a taimaka min da amsa ko. Nagode.

Amsa:

Wa alaikum assalam Za’a raba abin da ta bari gida :6, sai a baiwa mahaifiyarku kashi:1, in har akwai namiji a cikin ku sai a baku ragowar kashi biyar din ku raba duk namiji ya dau rabon Mata biyu. ‘yan uba ba sa yin gado mutukar akwai namiji a cikin shakikai.

Allah ne mafi sani .

Allah ne mafi sani

 

Hukuncin Faxin ‘Juma’at Mubarak’

Tambaya:

Assalamu Alaikum. Dr ko ya halatta Musulmi yayi wa dan’uwansa murna da zagayowar juma’a ta hanyar sako a wayar sailula kamar ace JUMA’A KAREEM ko JUMA’A MUBARAK? Allah yaqara sani.

Amsa:

Wa’alaikum assalam, Akwai malaman da su ka hana hakan, suna ganin ba shi da asali a addini, Amma abin da yake zahiri hakan ya fi kama da al’ada, wannan yasa haramta shi yake bukatar Nassi, tun da babin al’adu da mu’amaloli a bude yake, sai abin da sharia ta haramta. Duk Wanda yake yi ba tare da ya riya cewa ibada ba ce hana shi ko bidi’antar da aikinsa yana da wuya, kamar yadda Ibnu Uthaimin ya yi nuni zuwa haka a fatawar da aka yi masa.

Sai dai, duk da haka ya kamata kar Musulmi ya zamar da shi al-adarsa kowace juma’a, don kar wasu su fahimci ibada ne.

Allah ne mafi sani.

 

Fatawar Rabon Gado (47)

Tambaya:

Assalamu Alaikum Dr. Mutum ne ya rasu bai yi aure ba, ya bar mahaifiyarsa da yayarsa uwa daya uba daya da kuma kanwa mace daya wacce suka hada uba daya, to ya rabon gadonsa zai kasance? .nagode

 

Amsa:

Wa alaikum assalam, Za’a raba abin da ya bari gida: 5, a bawa babarsa kashi: 1, sai ‘yar’uwarsa shakikiya ta dau kashi: 3, wacce suka hada uba daya kawai ta dau kashi dayan da ya rage.

Allah ne mafi Sani.

 

A Cikin Sahabbai Wane Ne Sahabi, Xan Sahabi, Jikan Sahabi, Baban Sahabi?

 

Tambaya:

Assalamu alaikum, don Allah akwai sahabin da kakansa sahabi ne, babansa sahabi, xansa kuma sahabi ?, ina son karin bayani malam.

Amsa:

Wa alaikum salam, To malam sahabin da yake kakansa sahabi, dansa sahabi, babansa sahabi, shi ne: Abdurrahman dan Abi-bakr bn Abi Khuhafah kamar yadda Ibnu Salah da Ibnul-jauzy suka ambata. Saboda mahaifinsa Abubakar sahabi ne, hakanan kakansa Abu khuhafah shi ma sahabi ne sannan dansa Muhammad  sahabi ne, Ibnu Hajar yana cewa: Ba mu san mutum hudu da ‘ya’yansu wadanda suka ga  Annabi (SAW) ba sai wadannan.

Abin da yake nufi shi ne: Muhammad da mahaifinsa Abdurrahman da kakansa Abubakar da kakansa na biyu Abu-kuhafah dukkansu sun ga Annabi (SAW) don haka su kadai suka samu wannan darajar, Allah ya kara musu yarda .

Don neman karin bayani duba tarjamar Muhammad Bn Abdurrahman Bn Abi-bakr Bn Abi-khuhafah a Usudul-gabah a lamba ta: 6083.

 

Fatawar Rabon Gado (48)

Tambaya:

Assalamu alaikum. Malam Tambaya akan rabon gado. Mutum ne ya mutu yabar Mahaifiya, mata, kanne shaqiqai, li’ummai, da kuma li’abbai Babu da ko ya. Yaya Rabon zai kasance?

Amsa:

Wa alaikum assalam, Za’a raba abin da ya bari gida:12, a bawa mahaifiyarsa kashi:2, matarsa kashi uku, ‘yan’uwansa li’ummai kashi:4, Sai shakikai su kwashe ragowar kashi: 3.

Allah ne Mafi sani.

 

Idan Direba Ya Kashe Mutane Bakwai, Yaya Kaffararsa?

Tambaya:

Assalamu alaykum tambayata anan shine idan tsautsayi yasa Kai ajalin rai bakwai da motarka, idan zakai axumi na kaffara nawa zakai?

Amsa:

To dan’uwa kisan kuskure yana wajabta abubuwa guda biyu:

1- Diyya wace dangin wanda ya yi kisan za su bayar ga dangin wanda aka kashe da kuskure, sai dai in sun yafe.

2- Kaffara, wacce zai ‘yanta kuyanga, in bai samu ba sai ya yi azumin wata biyu, kamar yadda aya ta 92 a Suratunnisa’i take nuni zuwa hakan.

Idan sama da mutum daya suka mutu a mota, ya wajaba ga Driban motar ya yiwa kowa kaffara kuma danginsa su biya diyya, mutukar shi ne sababi a hadarin, kamar ya zamana ya wuce danja ko kuma ya yi gudun da ya zarta ka’ida, ko burkinsa ya lalace amma ya ki gyarawa, ko wani abu makamancin haka wanda yake nuna sakacin Direba, ko wuce ka’idarsa.

Idan hadari ya faru wasu suka ji ciwo saboda sakacin Direba ko wuce ka’idarsa, sai suka mutu daga baya, danginsa za su biya diyyarsu kuma zai yiwa kowa kaffara, ko da kuwa bayan shekaru biyar ne da faruwar hadarin, saboda duk dalilin da yake kaiwa zuwa abu, to yana dai dai da abun.

Don neman Karin bayani duba: Al’inaya 1\116, Madalibu Uli-Annuhaa 6\147 da kuma Fataawa Allajnah Adda’imah 23\352.

Allah ne mafi sani.

 

Fatawar Rabon Gado (49)

Tambaya:

Assalamu alaikum malam ina da tambaya. Magidanci ne ya rasu. ya bar  Yara 12, maza 8 mata 4 da kuma iyalinsa. Biyu, uwargida tana da Yara 9 amarya tana da Yara 3, to amarya ta yi aure, ya rabon gadon chike?, Allah chi karama malam lafiya amin

Amsa:

Wa alaikum assalam, Za’a raba abin da ya bari gida:8, a bawa matansa kashi daya su raba, ragowar kashi bakwan sai a bawa ‘ya’yansa su raba, duk namiji ya dau rabon mata biyu.

Allah ne mafi sani.

 
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: