Connect with us

KIWON LAFIYA

Amfanin Man Zaitun Ga Rayuwar Al’umma

Published

on

Man zaitun dai mai ne da ake amfani da shi tun zamanin Kaka da kakani musamman a wurare da aka san amfanin shi. A wasu sassan ana amfani da man a abinci ko a shafa yayin da aka sami wani rauni. Manazarta a fannin kiwon lafiya sun bayyana wasu daga cikin alfanun man zaitun ga rayuwar alumma, wanda suka hada da: 1. Man zaitun na magance cutar kansa (cancer): Kamar yadda wata kungiya masu kula da fannin kiwon lafiya a kasar Espaniya (Spain) suka tabbatar man zaitun na matukar taimako wajen rage barazanar cutar kansa saboda da sinadarin “antiodidants” da ya kunsa. 2. Man zaitun na kuma magance cutar suga (diabetes): Kwararru a fannin yaki da cutar sikari sun tabbatar da amfani da man zaitun na rage yiwuwar kamuwa da cutar sikari mai lamba 2 wanda ke da matukar hatsari ga rayuwar alumma saboda da wasu sinadaran da shi man zaitun ya kunsa. 3. Man zaitun na kuma kone kitse: A wani nazari da aka gudanar a jami’ar Nabara dake garin Las Palmas dake kasar Espaniya (Spain) ya tabbatar da duk mai amfani da man zaitun wajen cin man, da cewa man zai taimaka ma shi ta hanyar kone akasarin kitse da zai iya illa ga

rayuwar mutumin. Kana har ila yau hakan zai samarwa mai amfani da man natsuwa a kwkkwalwar shi. 4. Man na kuma gyara fata tare da samar da sumar gashi. Masana sun tabbatar da amfani da man na zaitun na taimakawa fatar jikin bil’adama saboda yana dauke

da sinadarin bitamin A da Kuma bitamin E wanda dukkannin su suna taimakawa fata. Har ila yau kuma sun bayyana man zaitun da yana taimakawa wajen samar da sumar kai. 5. Man zaitun na kuma magance cutar ciwon zuciya: An bayyana

manazarta suka gudanar sun tabbatar da cewa man na zaitun na taimakawa wajen rage barazanar cutar ciwon zuciya musamman ga tsofaffi. Wannan na nuna cewa amfani da man na zaitun zai taimaka gaya wajen kare lafiyar mutum

 
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: