Connect with us

KASASHEN WAJE

An Ceto Bakin Haure 211 Daga Tekun Libya

Published

on

Wasu kungiyoyin jinkai sun ceto karin wasu bakin haure a su 81 ruwan Lybia a ranar Lahadi, lamarin da ya kai adadin mutanen da aka ceto su daga teku tun ranar Juma’a zuwa 211. Kungiyar “Doctors without Borders” da hadin gwiwar kungiyar SOS Mediterranean sun yi aikin ceton ne da wani jirgin ruwa mai dauke da tutar KasarNorway mai suna Ocean Biking.

Akasarin mutanen da aka ceto tsakanin kwanaki uku, ‘yan maza ne daga Kasar Sudan, ciki har da mutane 81 da aka samo su a cikin wani karamin kwalekwalen roba. Ma’aikatan jirgin ruwan “Ocean Binking” da suka shedi al’amarin sun ce mutanen da suke cikin kwalekwalen robar da ya sace, sun barke da murna a lokacin da su ka ga masu ceton.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: